Yayin da watan Ramadan mai alfarma ya zo karshe, mu a Kasuwancinduniya muna mika sakon taya murna da fatan alheri ga dukkan masu karatunmu, abokan hulda, da al’ummar Musulmi baki daya bisa zagayowar babbar Sallar Eid-el-Fitr.
Wannan lokaci ne na godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ikon da Ya ba mu na kammala ibadun watan Ramadan, da kuma darussan hakuri, juriya, tausayi da kyautatawa da muka koya a wannan wata mai albarka.
Muna kira ga kowa da kowa da ya ci gaba da rike kyawawan dabi’u da aka koya a watan Ramadan, tare da inganta zaman lafiya, hadin kai, da fahimtar juna a tsakanin al’umma domin cigaban kasa baki daya.
Mu a Kasuwancinduniya, za mu ci gaba da jajircewa wajen isar da sahihan labarai, masu ma’ana da tasiri, domin wayar da kai da karfafa gina al’umma mai inganci.
Muna rokon Allah Ya karbi ibadunmu, Ya sanya mana albarka, Ya kuma sa mu kai ga ganin wasu lokuta irin wannan cikin koshin lafiya da wadata.
Barka da Sallah!
Sa hannu:
Gudanarwa
Kasuwancinduniya



















