Daga; Bashir Bello, Abuja
AKALLA ɗalibai 75 daga al’ummar Oworo da ke Jihar Kogi sun amfana da shirin tallafin karatu na miliyoyin naira wanda kamfanin Simintin Dangote ta aiwatar a matsayin wani ɓangare na shirinta na ɗaukar nauyin al’umma (CSR).
Wannan ya kawo jimillar tallafin karatu izuwa guda dari da ashirun da biyar (125) wanda kamfanin ta bayar tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026.
Shirin tallafin karatu, wanda Kamfanin Simintin Dangote ta fara, yana da nufin faɗaɗa sawun nauyin al’umma na kamfanoni (CSR) a faɗin yankin Oworo, wanda ya ke da fiye da manyan al’ummomin yankuna guda biyar na Jakura, Oyo, Iwaa, Apata, da Obajana.
Wakilin Daraktan Masana’antar, kamfanin ta Obajana Plant, Mista Ademola Adeyemi, ya bayyana cewa yayin da dalibai 50 suka ci gajiyar shirin a shekarar 2025, adadin ya karu zuwa dalibai 75 a shekarar 2026.
Ya ce, “an tsara wannan shiri ne don bayar da agajin kudi ga dalibai yayin da ake rage nauyin kudaden karatu ga iyaye da masu kula da su.
“Karin ya kara nuna jajircewar Kamfanin na zuba jari a fannin bunkasa jarin dan adam da kuma tallafawa burin ilimi na matasa a cikin al’ummomin da ke karbar bakuncin kamfanin da kuma yankunan da ke makwabtaka da su.
Taron ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki daga al’ummomin da ke karbar bakuncin taron, cibiyoyin Gwamnati, da kuma kungiyar ci gaban Oworo.
A jawabinsa na bude taron, Shugaban kungiyar ci gaban Oworo, Mista Ibrahim Adoga, ya nuna matukar godiya ga kamfanin Simintin Dangote ta Obajana saboda ci gaba da zuba jari a ci gaban al’umma.
Ya yaba da ayyukan ci gaba daban-daban da kamfanin ta gudanar a fadin al’ummomin da ke yankin da kuma yankunan da ke karkashin kulawarsa, sannan ya ambaci kaddamar da rijiyoyin burtsatse guda 5 da aka haƙa a cikin al’ummomi biyar a Oworoland a shekarar 2025, yayin da aka haƙa ƙarin guda huɗu a shekarar 2026.
Mista Adoga ya yaba wa shugabannin Kamfanin, musamman Aliko Dangote, babban Shugaban Masana’antar, da ma’aikatan saboda yadda shirin tallafin karatu ya zama gaskiya.
Ya bayyana karuwar waɗanda suka ci gajiyar shirin daga ɗalibai 50 zuwa 75 a matsayin wani abin yabo da zai rage wa iyaye da waɗanda ke ƙarƙashinsa nauyi sosai daga matsalolin kuɗi da suka shafi manyan makarantu.
Ya yi kira ga shugabannin gargajiya, ƙungiyoyin matasa, mata, da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafawa tare da kare Kamfanin Simintin a matsayin wani kadara mai daraja ga al’umma.
A cewarsa, jajircewar kamfanin ga ilimi mai ɗorewa yana ƙirƙirar damammaki masu canza rayuwa ga ɗalibai da yawa marasa galihu a yankin Oworo.
Jagororin da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun gabatar da saƙonnin fatan alheri da dama.
Da ya ke jawabi a madadin iyaye, Alkali Ibrahim Eleson Denja, ya bayyana godiyarda ga kamfanin saboda ci gaba da shirin bayar da tallafin karatu da kuma yin tasiri mai kyau ga ci gaban ilimi a yankin Oworo.
Masu jawabi sun yaba wa kamfanin bisa ga tsarin da ta ke bi wajen kula da bukatun al’umma da kuma jajircewarta wajen bunkasa ci gaba mai dorewa ta hanyar ilimi.
Da take gabatar da godiya ga wadanda suka amfana, Miss Oheda Faith Helen, daliba a fannin Biochemistry Kogi State Polytechnic, Lokoja, ta bayyana matukar godiyarta ga kamfanin ta Obajana saboda kyautar tallafin karatu.
Ta bayyana cewa wannan matakin zai taimaka wa dalibai sosai wajen cimma burinsu na ilimi da kuma rage nauyin kudi ga iyalansu.
An kammala taron da farin ciki kana da addu’ar rufe taro karkashin jagorancin mai girma Ezekiel Kehinde, tare da rera wakar “We Are Grateful Lord,” wanda ke nuna godiya ga wadanda suka amfana da kuma mutanen Oworo saboda ci gaba da goyon baya da fatan alheri na kamfanin Simintin .
Shirin bayar da kyautar tallafin karatu na makarantun gaba da sakandare na Oworo na shekarar 2026 ya kara karfafa jajircewar kamfanin Simintin Dangote ta Obajana wajen ci gaban al’umma mai dorewa ta hanyar ilimi.
Hakazalika, ta hanyar haɓaka adadin waɗanda za su ci moriyar tallafin karatu da jimillar ƙimar tallafin karatu, kamfanin ta nuna jajircewarta na ƙarfafa matasa, da haɓaka ƙwararrun ilimi, da kuma ƙarfafa dangantakarta da al’ummomin masu masaukin baki da ke yankin Oworo.
Wadanda suka halarci taron sun hada da: Engr. E. O. Olaitan Femi, jami’in ma’adinai na tarayya, Mrs. Onimode O. A., darakta a ma’aikatar albarkatun kasa ta Jihar Kogi da kuma Cif Ibrahim Adoga, shugaban kungiyar bunkasa Oworo (ODA).
Sauran sune: wakilin Olu of Oworo, HRH Alhaji Seidu Adoga Aliyu, Obaro na al’ummar Omuwa. Cif K.A. Mahmoud, Shugaban Kwamitin Asusun Tallafawa Ilimi na Oworo (OWEEEF), Malam Abubakar Abdulkadir, Sakataren Kwamitin OWEEF, Hajiya Ayisat Abdul, mamban kwamitin, OWEEF, Cif G. A. Abdullahi, memba na kwamitin, OWEEF, Majistare Lele Ibrahim, Alhaji Haruna Aliyu da Cif Ezekiel J. K., Shugaban JDA na kasa.



















