Daga Bashir Bello.
Rukunin Kamfanonin Dangote da Gwamnatin Jihar Kano na kara karfafa dangantaka domin bunkasa harkokin kasuwanci da shirye-shiryen jin kai a cikin jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da mahalarta ke ci gaba da tururuwa zuwa rumfar kamfanin a baje kolin kasa da kasa na Kano karo na 46, domin ganin sabbin kayayyakin kirkira da aka nuna.
Kwamishinan Zuba Jari da Kasuwanci na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, ya shaida wa manema labarai a wajen baje kolin cewa jihar na kara karfafa hadin gwiwa da Rukunin Dangote tare da duba sabbin hanyoyin hadaka.
“Hadin gwiwa da Rukunin Dangote zai karfafa masana’antu ta hanyar kasuwanci a Kano. Ta hanyar hada manufofin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, muna samar da damammaki don ci gaban kasuwanci a jihar Kano.” Ya ce.
Ya yaba wa kamfanin bisa jajircewarsa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya, musamman goyon bayan da yake bai wa baje kolin kasuwanc




















