Daga Bashir Bello












An kafa tarihi a wajen bikin kaddamar da shirin “Renewed Hope Empowerment Programme”, inda Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajuddeen, ya kaddamar da fara wasu manyan ayyuka don ci gaban alumma tare da raba motocin SUV, kayan aikin noma, kayan tallafi, da kuma kayyayakin sanaoie a matsayin wani bangare na ayyukan mazabarsa.
Wannan biki mai kayatarwa da aka gudanar a Zariya ya jawo manyan baki daga sassa daban-daban, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya; Ministan Muhalli; Balarabe Abbas, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman, Sarkin Hadejia daga Jihar Jigawa; ‘yan Majalisar Wakilai; da kuma sarakunan gargajiya, wadanda duk suka halarci wannan gagarumin taro.
Hotuna: Bashir Bello Dollars

















