Daga; BASHIR BELLO, Majalisa Abuja.
DAN Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Katagum daga Jihar Bauchi, Honarabul Auwalu Abdu Gwalabe ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya rataya hakkin kula da lafiyar mutane da dukiyoyin su a wayun shugabanni.
Da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa dake Majalisar Tarayya Abuja, Dan Majalisar ya nunar da cewa Gwamnati tana iya bakin kokarin ta wajen ta sauke nauyin daya rataya a wuyan shugabannin ta.
Acewar sa, wajibi ne shugabanni wadanda ke Jagorantar al’umma da su tabbatar da sun dauki nauyin daya rataya a wuyan su wanda ya ke hakki ne na al’umma musamman domin kula da kare lafiyar mutanen da suke Jagoranta tare da dukiyoyin su.
Ya kare da cewa Kasar Najeriya musamman a Arewacin Najeriya na fuskantar barazanar kalubalen tsaro duk da cewa Gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen samar da kudade da kayan aikin da ake bukata amma lamarin na yawan daukar sabon salo




















