Daga; BASHIR BELLO, Majalisa Abuja.
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Faskari, Kankara da Sabuwa, dake Jihar Kataina, Honarabul Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki ya bayyana cewa inganta rayuwar al’ummar sa shi ne babban ginshikin samun nasarar da ya sanya a gaba.
A wani zantawarsa da manema labarai a garin Abuja, Hon. Shehu Tafoki ya nunar da cewa ba shi da wani babban burin daya sanya a gaba wanda ya wuce na al’ummar da yake wakilta.




Acewar sa, ziyarar kaddamar da ayyuka wanda Gwamnan Jihar, Dakta Dikko Rada ya kai a yan kwanakin a yankin sa ya nuna irin cigaban da ake samu duk da irin kalubalen matsalar taso da suke fuskanta.
Ya kara da cewa a bisa irin wannan yunkurin na tabbatar samun ci gaba ne ya sanya Gwamnan Jihar ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka tare da mika gaisuwa ga Hakimai, Dakatai da manyan yan Siyasa masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin da yake wakilta.
Ya ce, “tun daga lokacin da nake Dan Majalisar Jiha har izuwa lokacin da na zama na Tarayya, kokarin da nake yi duk bai wuci na yunkurin tabbatar da jin dadi da walwalar al’ummar da nake wakilta ba kuma zuwan Gwamnan mazaba ta ya nuna irin cigaban da ake samu.
“Mazabar da nake wakilta ta kasance mafi girma daga cikin duka mazabun da muke da su a Jihar Kataina amma kokarin da nake shi ne barin wani abu wanda al’umma zasu rika amfani da shi ko tunawa da kai ko bayan ka bayar mulki.
“Hakan yasa nayi kokarin gyara wasu Makarantun, ba da tallafin Noma ga mutane 880 wanda 400 daga ciki an ba su karin jari ne, wasu POS, na raba mashina 71, motocin Yan kumbula 9 da 206 5, sannan da kekunan Dinki ga mata 115 tare da injin din nika 205.
“Sannan sannin mahimmancin Noma ga Manoma yasa na raba buhuhunan Takin noman Rani, kana na samarwa matasa da dama wasu ayyukan yi Kuma a yanzu haka akwai matasa 100 daga cikin mutanen da suke neman aikin Soji da sauran ayyukan kayan Sarkin wadanda nake kokarin tabbatar da samar musu aikin.” Inji shi
Hakazalika, Dan Majalisar ya yi nuni da cewa Gwamnan Jihar Kataina na daga cikin mutanen da suke samun hadin kai dari bisa dari daga wajen Yan Majalisar Tarayyarsa saboda baki daya Wakilai 15 dake Majalisar na kokarin tabbatar sun goya masa baya a duk lokacin da yake bukatar hakan.
A karshe , Honarabul Shehu Dalhatu Tafoki, ya jan hankalin sauran Yan uwansa Yan Majalisar da su kasance masu tawali’u tare da yin amfani da damar da suka samu wajen tabbatar da sun bar wani mai tasiri ga rayuwar al’ummar da suke wakilta wanda za a rika tunawa da su ko bayan ba su.




















