
Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.
Shugaban Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai Kan Sauye-sauyen Bangaren Wutar Lantarki, Hon. Ibrahim Al-Mustapha Aliyu, ya bukaci karin jajircewa daga dukkan masu ruwa da tsaki, musamman kamfanonin samar da wuta da na rarrabawa, domin tabbatar da nasarar tsarin kason raba hannun jari a bangaren wutar lantarkin Najeriya.
Yayin da yake jawabi a wani zaman bincike na kwamitin kan sauye-sauyen da suka faru daga shekarar 2007 zuwa 2024, Hon. Aliyu ya jaddada cewa da cikakken sadaukarwa da jajircewa, bangaren wutar lantarki na Najeriya zai iya kaiwa matakin da ya dace.
Ya tunatar da masu ruwa da tsaki cewa wakilan majalisar 360 suna wakiltar sama da mutane miliyan 200, wadanda ke da hakkin sanin abin da ke faruwa da kuma samun mafita ga matsalolin da suka dade suna addabar bangaren wutar lantarki.
A headkwatan mazabata dake Rabah a Jihar Sakwato, mun Kai Shekaru Takwas bamu da Wutan lantarki kuma muna karkashin KEDKO ne dake Jihar Kaduna” Acewar Hon. Al-Mustapha.
“Wannan Kalubalen rashin Wutan lantarki yana shafan Dukkan yan majalisun a mazabar su, Shi yasa muke son ayi gyara” Inji Hon. Al-Mustapha
Haka zalika, yayin da ya bayyana a gaban kwamitin, Darakta Janar na Hukumar Kula da Kadarorin Jama’a (BPE), Mista Ayodeji Ariyo, ya kare lokacin da aka aiwatar da sauye-sauyen, yana mai cewa da ba a yi su ba, da bangaren wutar lantarki ya durkushe, yana kwatanta halin da ake ciki da yadda kamfanin sadarwa na NITEL ya kare a baya.
“Inason in tabbatar muku cewa da baayi wannan sauyin ba, da Bangaren Wutan lantarki ya Shiga Matsalar da NITEL ta Shiga Kafin a saka hannun Kari” Inji Mr. Ariyo.
Yayin da suke zantawa da manema labarai, wasu wakilan kamfanonin samar da wutar lantarki ta ruwa suma sun goyi bayan sauye-sauyen.
Bashir Sufyan da Umar Shehu Hashidu daga kamfanin Mabon Limited, masu kula da madatsar Dadinkowa da ke jihar Gombe, sun bayyana cewa tsarin kason raba hannun jari yana haifar da sakamako mai kyau, kuma da ci gaba da goyon bayan gwamnati, suna da yakinin samun karin nasarori a gaba.




















