
Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja
Wata babbar tawaga daga kananan hukumomin Bagwai da Shanono a Jihar Kano ta kai ziyarar girmamawa ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin Maliya.
Tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Farook Lawan, ne ya jagoranci tawagar wadda ta kunshi matasa, dattijai da mata daga kananan hukumomin Biyu.
Manufar ziyarar ita ce nuna godiya da goyon baya ga Sanata Barau Jibrin bisa irin tallafi da shirye shiryen karfafa al’umma da ya dade yaka aiwatarwa ba kawai a Bagwai da Shanono ba, har ma a fadin jihar Kano baki daya.
A cikin jawabin sa, Hon. Farook Lawan ya yaba wa Sanata Barau bisa matakan da ya dauka wajen dawo da zaman lafiya, Hadin kai da kwanciyar hankali a lokacin da yankin ya fuskanci kalubalen tsaro. Ya bayyana wasu daga cikin ayyukan da Sanatan ya gudanar a mazabarsa, ciki har da gina rijiyoyin burtsatse, makarantu, asibitoci, hanyoyi, bayar da tallafin karatu, samar da ayyukan yi, raba abinci, taki, motoci da kuma kudi kai tsaye ga al’umma.
Tawagar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga takarar Sanata Barau Jibrin a matsayin Gwamnan Jihar Kano a zaben 2027, da kuma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu amatsayin Shugaban Kasan Nigeria a Zaben 2027 Haka kuma, sun bayyana Hon. Farook Lawan a matsayin zabinsu wanda zai wakilci mazabar tarayya ta Bagwai da Shanono a Majalisar Wakilai a shekarar 2027.
Da yake mayar da martani, Sanata Barau Jibrin ya nuna godiya bisa wannan ziyara da kuma goyon bayan da ya dade yana samu daga al’ummar yankin. Ya jaddada kudirinsa na ci gaba da taimakawa al’umma ta hanyar aiwatar da ayyuka da manufofi masu tasiri kai tsaye a rayuwar jama’a. Haka kuma, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da daukar matakai daban daban domin inganta tsaro a yankin.
Ziyarar ta kasance alamar sabuwar alaka mai karfi tsakanin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da al’ummar Bagwai da Shanono, tare da fatan samun ci gaba mai dorewa a Jihar Kano.




















