• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Labarai

Matsalar da ke janyo yawan ɓarin ciki da mata ba su sani ba

December 13, 2025
in Labarai
Reading Time: 3 mins read
0
Matsalar da ke janyo yawan ɓarin ciki da mata ba su sani ba
0
SHARES
10
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Yadda RH Incompatibility ke shafar ciki
Akwai wasu matsalolin lafiya da mata ke fuskanta a cikin ɗaukar ciki da haihuwa da ake gani kamar ƙananan abubuwa ne, amma sukan zama babbar barazana ga iyali.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan matsalolin ita ce ‘RH incompatibility’ – wani yanayi da ke faruwa idan jinin uwa da na jariri ba su jitu ba kamar yadda Dr Bahijja Faruk, ƙwararriryar likitar mata ta shaida wa BBC.

Karanta HakananPosts

Ƙarfafa Kamfanoni Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Katsina, Ya Ƙarfafa Tsaro Inji Gwamna Radda

Mauludi: Sabunta Alkawarinmu ga Zaman Lafiya, Tausayi da Jinƙai

Mauludi: Ku yi addu’ar farfaɗowar tattalin arziki da inganta tsaro — Ashiru ya roƙi al’ummar Musulmi

Wannan matsala in ji ta na janyo zubewar ciki akai-akai da haihuwar jarirai marasa ƙarfi ko marasa lafiya ko ma mutuwar jarirai kafin ko bayan haihuwa.

Ta ƙara da cewa, “A cikin al’ummominmu inda mutane ke da ƙarancin ilimin kiwon lafiya, musamman batun RH, mata da dama na fuskantar ɓari ba tare da sanin musabbabin matsalar ba. “Mene ne rashin jituwar jini (RH incompatibility)?
Dr Bahijja ta bayyana cewa, RH wani sinadari ne da ke cikin jinin mutum. Yana zuwa a nau’i biyu ne in ji ta da suka haɗa da:

RH Positive (RH+)
RH Negative (RH−)
Saboda haka rashin jituwar jinin uwa mai ɗauke da juna biyu da na jariri, shi ake kira da ‘RH-incompatibility’.

“Idan mace tana da jinin RH-negative, mijinta kuma yana da RH-positive, jaririn da za ta haifa zai iya gado jinin mahaifi. Wannan na iya janyo matsala domin jinin uwa ba zai jitu da jinin jaririn ba,” in ji likitar. Abin da ake nufi a nan shi ne jinin RH-negative ba ya jituwa da na RH-positive.”

“Dalilin haka ne jikin uwa za iya ɗaukar jinin jariri a matsayin abokin gaba, ya ƙirƙiri ƙwayoyin kariya da ke kai farmaki ga jinin jaririn, wanda hakan ke haifar da abubuwa kamar haka:

Zubewar ciki
Rashin girman jariri cikin lafiya,
Lalurar Jaundice mai tsanani,
Ko mutuwar jariri cikin mahaifa.
Mene ne ke haifar da rashin jituwar jini?
Likitar ta ce wannan matsalar na faruwa ne idan jinin uwa da ke Rh-negative ya haɗu da na jariri da ke Rh-positive wanda ke faruwa yayin ɓari ko haihuwa ko ɗaurin ciki mara kyau (ectopic pregnancy), ko gwaje-gwajen ciki da ake yi da allura da dai sauransu.

Yadda RH Incompatibility ke shafar ciki Dr Bahijja ta ce wannan lamari na iya shafar ciki ta fanni daban-daban.

Ga jariri, zai iya

Lalata jinin jariri har ya kai ga mutuwa
Shawara mai tsanani (Jaundice)
Rashin isasshen jini (anemia)
Hydrops fetalis (Wannan wata matsala ce mai tsanani a cikin ciki, inda ruwa ke taruwa a kalla a sassan jiki biyu na jariri, kamar cikin ƙirji (pleural effusion) da zuciya (pericardial effusion), ko ƙarƙashin fata (edema).
Rashin girman jariri
Mutuwar jariri a ciki ko bayan haihuwa
Ga Uwa kuma, ta ce

Ɓari akai-akai
Ciki ba ya tsayawa
Cikin da ke ɗaukar tsawon lokaci ba tare da haihuwa ba
Damuwa da fargaba
“Shekarata 10 da aure, sau shida ina ɓari’ lokacin da Maryam ta auri mijinta shekaru goma da suka gabata, burinta bai wuce ta haihu ta riƙe ɗanta ko ‘yarta ba amma har yanzu burin na ta bai cika ba.

Cikin shekaru goma da aurensu, Maryam ta yi ɓari sau shida, ba tare da ta taɓa gane dalilin ba.

“Na fara daukar ciki ne a shekarar farko bayan aurenmu,” in ji Maryam. “Amma cikin bai kai watanni biyu ba ya zube. Na yi tunanin wata matsala ce ta wucin gadi. Bayan haka kuma na sake ɗauka, har sau biyar duk suna zubewa.”

Shekaru suna tafiya, damuwa na ƙaruwa, magunguna da addu’o’i sun yi yawa, amma ba wani sauyi. Sai dai ɓarin cikin da take samu akai-akai.

Sai daga baya da ta sake ɓari, sai wata ƙawarta take faɗa mata batun Rh -incompatibiliy, shine ya sa ta faɗawa mijinta sai suka je babban asibiti akwai gwada su.

“Asibitin gaskiya na da tsada, amma kuma sun wayar da kanmu kan wannan batu kuma sun mana maganar alluran rigakafin da ya kamata mace mai Rh- ya kamata ta karɓa bayan ɓari ko haihuwa, abin da bata taɓa ji ko karɓa ba.” in ji ta.

Yanzu dai ta ce sun je asibiti kuma sina fatan komai zai yi dai-dai daga yanzu.

Mene ne rigakafin Anti-D (RhoGAM)
Likitar ta ce alluran rigakaifin da ya kamata a yi wa mace mai RH- da ta ɗauki ciki ta haihu ko ta samu ɓari da zai kareta daga wani ɓarin idan ta samu wani cikin shi aka kira da Anti-D (RhoGAM)

“Idan har ba ta karɓi wannan rigakafin ba, jikinta na iya samar da ƙwayoyin halitta na kariya wato antibodies kenan.

Wadannan antibodies din suna kasancewa a cikin jini suna aiki ta hanyar;

Kai farmaki ga jinin jaririn idan wani sabon ciki ya shiga.
Lalata jinin jaririn tun kafin ya girma.
Ɓari sau da yawa koda kuma jaririn ya fara girma.
Ana bayar da rigakafin ne duk

Bayan ɓari
Cikin awanni 72 bayan haihuwa idan jariri Rh-positive ne
Lokacin da aka yi tiyata ko wani abu da zai zubar da jini
A makonni 28 na ciki (domin kariya) Credit:BBC Hausa

Previous Post

Dangote Ya Kaddamar da Tallafin Karatu na Naira Tiriliyan Daya

Next Post

Matan da suka fi shahara a 2025

Related Posts

Ƙarfafa Kamfanoni Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Katsina, Ya Ƙarfafa Tsaro Inji Gwamna Radda
Labarai

Ƙarfafa Kamfanoni Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Katsina, Ya Ƙarfafa Tsaro Inji Gwamna Radda

September 6, 2026
Mauludi: Sabunta Alkawarinmu ga Zaman Lafiya, Tausayi da Jinƙai
Labarai

Mauludi: Sabunta Alkawarinmu ga Zaman Lafiya, Tausayi da Jinƙai

August 26, 2026
Mauludi: Ku yi addu’ar farfaɗowar tattalin arziki da inganta tsaro — Ashiru ya roƙi al’ummar Musulmi
Labarai

Mauludi: Ku yi addu’ar farfaɗowar tattalin arziki da inganta tsaro — Ashiru ya roƙi al’ummar Musulmi

August 25, 2026
RUNDUNAR YAN SANDAR JIHAR KADUNA SUN YI ALLAH WADAI DA KISAN GILLA DA AKAYI MA WASU MATAFIYA, SUN KAMA MUTUM 6 KAN KASHE MUTUM 2 MARASA LAIFI
Labarai

RUNDUNAR ‘YAN SANDA KADUNA TA AMSA BIDION DA YA YADU, TA GARGADI JAMI’AI KAN CIN HANCIN DA HALAYEN DA BA DAI DAI BA

August 18, 2026
Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Sakatarorin Dindindin Hudu
Labarai

Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Sakatarorin Dindindin Hudu

August 5, 2026
Gwamna Yusuf Ya Tabbatar da Aiwatar da Bin Dokokin Zirga-zirga a Kano
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Tabbatar da Aiwatar da Bin Dokokin Zirga-zirga a Kano

August 4, 2026
Next Post
Matan da suka fi shahara a 2025

Matan da suka fi shahara a 2025

NNPC Ltd Ta Shawo Kan Matsalar Lalacewar Bututun Escravos–Lagos

NNPC Ltd Ta Shawo Kan Matsalar Lalacewar Bututun Escravos–Lagos

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

Shugaba Tinubu Ya Karɓi Rahoton Kuɗi Na NNPC Na Shekarar 2025 Bayan An Tantance Shi

October 13, 2026
Auto Draft

Tallafin Karatu Da Jarin Sana’a: Yadda Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Al’ummar Jakura

October 8, 2026
Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Sakatarorin Dindindin Hudu

Ranar Malamai ta Duniya: Ba Za Mu Bar Malaman Katsina Su Yi Aiki Cikin Wahala Ba – Gwamna Raɗɗa

October 7, 2026
Gwamna Yusuf Ya Tabbatar da Aiwatar da Bin Dokokin Zirga-zirga a Kano

Gwamna Abba Yusuf Ya Saki Naira Miliyan 235 Domin Ƙarin Girma Ga Ma’aikatan SUBEB 18,984

October 7, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by CookieAdmin
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by CookieAdmin