Azima Bashir Aminu
Taron ƙungiyar tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika wato ECOWAS karo na 68 da aka faro yau Lahadi a birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya, ya mayar da hankali kacokan kan makomar ƙungiyar ta fannonin ƙawancen tsaro da haɓakar tattalin arziƙin ƙasashen ƙungiyar da kuma zaman lafiyar jama’arta. Tun a safiyar jiya Asabar wasu daga cikin shugabannin ƙasashen ƙungiyar ta ECOWAS suka kammala hallara a birnin Abuja inda shugaban Saliyo Julius Maada Bio da yanzu haka ke jan ragamar ƙungiyar ya fara jagorantar zaman.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, shugaba Bio ya ce a wannan taro, ECOWAS za ta yi nazari tare da sabunta hanyoyin tunƙarar matsalolin duk wasu matsaloli da ka iya tasowa a ƙasashen mambobinta da nufin samar da dabarun tunƙararsu cikin gaggawa.
Shugaban ya ce yankin na yammacin Afrika na ganin manya-manyan ƙalubale da ke buƙatar kulawar gaggawa don magance su, ciki har da matsaloli masu alaƙa da tsaro da suka dabaibaye yankin.
Bugu da ƙari shugaban na ECOWAS ya kuma cewa, zaman zai yi tattaunawa ta musamman game da juyin mulkin da aka fuskanta a ƙasashen ƙungiyar da suka ƙunshi na Guinea-Bissau da kuma na Benin da bai yi nasara ba.
A zaman wannan taro dai ana saran ECOWAS ta miƙa rahoton shekarar da muke shirin bankwana da ita ta 2025, ƙunshe da nasarori ko kuma ƙalubale kan matsalolin da yankin na yammacin Afrika ke fuskanta don sake nazartarsu a wani yanayi da za a yi daftarin tunƙarar sabuwar shekara. Credit : Radio France



















