

Daga Bashir Bello
A wani mataki mai muhimmanci na sulhu da ci gaban da zai dore, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Ltd.) ya sake jaddada aniyarsa na tabbatar da zaman lafiya, tattaunawa, da gudanar da ayyukan makamashi cikin gaskiya a yankin Ogoniland.
Wannan jaddadawa ta fito ne yayin wata ziyarar manyan jami’an Gwamnatin Tarayya zuwa yankin mai arzikin man fetur na Jihar Rivers a ranar Litinin.
A cewar wata sanarwa da Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPC Ltd., Andy Odeh, ya sanya wa hannu, Shugaban Kamfanin NNPC Ltd., Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana wannan ziyara a matsayin “alamar cigaba” da kuma “sabon salo” ga al’ummar Ogoni. Ya jaddada cewa ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nuni da sabon salo na haɗin gwiwa, girmama juna, da ɗaukar nauyin juna.
“Wannan ziyara na tabbatar da kudurin Gwamnatin Tarayya na zaman lafiya, tattaunawa, da dawo da amincewa,” in ji Ojulari. “A gare mu a NNPC Ltd., wannan sabon farawa ne da aka gina bisa haɗin kai, girmamawa da fahimtar juna.”
Ojulari ya bayyana tarihin wahala da yankin Ogoni ya fuskanta, yana mai cewa dole ne a fuskanci tarihi domin gina kyakkyawar makoma. Ya yaba da kwazon Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Komawar Ogoni ƙarƙashin jagorancin Farfesa Don Baridam da kuma Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, bisa jagoranci da ƙoƙarinsu na gina amincewa da haɗin kai.
Yayin da yake bayyana manufar NNPC Ltd. a yankin, Ojulari ya ce burin kamfanin ya wuce kawai hako mai. “Muna da yakinin cewa ci gaban makamashi dole ne ya kasance tare da kare muhalli da walwalar al’umma,” in ji shi.
A wani muhimmin ci gaba, Ojulari ya sanar da cewa matasa 30 yan asalin Ogoni sun samu tayin aikin dindindin daga NNPC Ltd., kuma za su fara aiki a watan Janairu na shekarar 2026.
“Wannan mataki ne mai ma’ana wajen samun Damar ci gaban al’umma,” ya ƙara da cewa.
Gwamnan Jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara, wanda ya halarci taron, ya nuna godiya ga Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa wajen warware matsalolin da suka dade suna damun yankin Ogoni. Ya bayyana cewa alkawuran da gwamnatin ta yi daga gine ginen ababen more rayuwa zuwa ilimi da samar da ayyukan yi, an Fara aiwatar Dasu.
“An tabbatar mana da ƙoƙarin gina amincewa, kafa Jami’ar Muhalli, asibitoci, filin masana’antu, da damar ayyukan yi,” in ji Fubara. “A yau, matasa maza da mata 30 ‘yan asalin Ogoni sun riga sun samu aikin NNPC Ltd.”
A madadin Shugaba Tinubu, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya yaba wa al’ummar Ogoni da Gwamnatin Jihar Rivers bisa haɗin kai da goyon bayansu. “Muna nan yau saboda mutanen Ogoni, domin mu nuna godiya a madadin Najeriya,” in ji Ribadu. “Jihar Rivers yanzu na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a ƙasar nan, kuma hakan ya samu ne saboda jagorancin gwamna nagari da kuma kyawawan halayen al’ummar Ogoni.”
Ogoniland, inda ke ɗauke da filin hako mai na OML-11, na ci gaba da kasancewa muhimmin ginshiƙi a fannin makamashi na Najeriya. Kamfanin NNPC Exploration and Production Limited (NEPL), reshen NNPC Ltd., ne ke gudanar da ayyukan a OML-11, wanda shi ne mafi girma a cikin filayen hako mai na ƙasa, inda Ogoniland ke da fiye da kashi 40 cikin 100 na adadin man da za a iya fitarwa.
Yayin da Gwamnatin Tarayya da NNPC Ltd. ke ci gaba da tattaunawa da al’ummomin yankin, wannan ziyara ta ranar Litinin na nuna sabon babi, warkarwa, ci gaba, da walwala ga kowa a yankin Ogoniland.



















