



Daga Bashir Bello
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kai ziyara zuwa Barikin Sojoji na Natsinta a ranar Alhamis, inda ya kaddamar da sabbin gidajen iyali guda 12 da aka gyara tare da gudanar da bikin Kirsimeti tare da al’umman Kiristoci da ke cikin barikin.
Gidajen da aka sabunta, wadanda ke cikin Corporal Below Quarters (CBQ), an sake fasalta su ne domin inganta rayuwar iyalan jami’an soji.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, Gwamna Radda ya yaba wa rundunar sojoji ta 17 Brigade bisa jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar. Ya danganta zaman lafiyar da ake morewa a Katsina da sadaukarwar jami’an tsaro da kuma hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro.
“Hadin gwiwarmu da rundunar soji na da matukar muhimmanci wajen cimma irin tsaron da muke morewa a yau,” in ji Gwamna Radda.
Haka kuma, ya yaba da sadaukarwar da iyalan jami’an soji ke yi, musamman matan aure da ke mara wa mazajensu baya a yayin da suke bakin aiki. “Ba tare da karfinku da goyon bayanku ba, da aikin zai fi wahala,” ya kara da cewa.
A matsayin wani bangare na bikin Kirsimeti, Gwamna Radda ya bayar da gudummawar naira miliyan goma (₦10,000,000) ga iyalan Kiristoci da ke zaune a cikin barikin, yana mai bayyana wannan kyauta a matsayin alamar hadin kai da kyakkyawar niyya.
Haka kuma, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan jaruman jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a yayin da suke bakin aiki domin kare rayuwar al’umma.
Da yake mayar da martani, Kwamandan Runduna ta 17, Birgediya Janar B.O. Omopariola, ya nuna godiyarsa ga Gwamna Radda bisa daukar nauyin aikin gyaran gidajen. Ya bayyana cewa wannan aiki ya yi daidai da tsarin sauya fasalin rundunar sojin Najeriya karkashin jagorancin Babban Hafsan Sojin Kasa.
“Wannan aiki zai inganta jin dadin dakarunmu da iyalansu. Yana nuna irin kishin da Gwamna ke da shi ga rundunar soji da kuma yadda yake daidaita da hangen nesanmu na gina rundunar soji mai kwarewa da juriya,” in ji Kwamandan.
Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar sabon wurin zama da su kula da gine ginen da aka gyara, tare da nuna kishin kasa da bin doka da oda.
Bayan kaddamar da aikin, Gwamna Radda ya gana da shugabannin al’umman Kiristoci a jihar Katsina.
Shugabannin addinin sun yaba da salon jagorancin Gwamnan na hada kan kowa, tare da alkawarin ci gaba da wayar da kan mabiyansu kan muhimmancin zaman lafiya da hadin kai tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, hafsoshin soji, shugabannin al’umma da mazauna barikin dukkansu suna cikin murna da godiya ga wannan kyakkyawar alherin da Gwamna Radda ya nuna.



















