Daga Ahmed Aliyu 

Kamfanin Dangote Cement Plc ya ninka kudin tallafin karatu da yake bayarwa ga al’ummomin da ke karɓar bakuncinsa a Gboko, Jihar Benue.
Shugaban Sashen Ayyukan Zamantakewa na Dangote Cement, Reshen Gboko, Dr. Johnson Kor, ya bayyana cewa kamfanin ya faɗaɗa shirin tallafin domin ya ƙunshi yawan masu cin gajiyar sa.
Daraktan Reshen Gboko, Injiniya Abhijit Dutta, yayin gabatar da takardar tallafin a Gboko, ya ce: “Tallafin karatun bana ya karu daga naira miliyan goma zuwa kusan naira miliyan talatin.”
Injiniya Dutta, wanda Shugaban Sashen Kudi, Olusegun Orebanjo, ya wakilta, ya bayyana cewa dalibai fiye da 230 ne za su amfana da tsarin ilimi na shekarar 2025.
Ya ce an faɗaɗa yawan al’ummomin da za su amfana daga Mbayion kawai zuwa wasu ƙauyukan hakar ma’adinai kamar Mbatur a gundumar Yandev, al’ummar Mbazembe a gundumar Ipav da kuma al’ummar Pass Brothers a ƙaramar hukumar Guma.
Injiniya Dutta ya ce kamfanin ba ya kallon al’ummomin da ke karɓar bakuncinsa a matsayin maƙwabta kawai, “amma a matsayin abokan haɗin gwiwa na ci gaba.”
Ya ƙara da cewa, “Dorewar wannan tsarin tallafin karatu ga ɗalibai marasa galihu amma masu cancanta na nuna yadda muke da ƙwarin gwiwa wajen tallafawa ilimi da ci gaban ɗan Adam.”
An gabatar da takardar tallafin ne a wani biki da ya haɗa da yaye matasa da suka kammala horo a wani shirin koyon sana’o’i da kamfanin Dangote Cement, Reshen Gboko, ya ɗauki nauyinsa, ƙarƙashin kulawar Hukumar Horas da Masana’antu (ITF).
A cewarsa: “A matsayin ƙarin shaida na wannan ƙuduri, an ƙara kuɗin tallafin zuwa Naira miliyan 28.8 a bana, tare da faɗaɗa shirin zuwa dukkan al’ummomi shida da ke karɓar bakuncin kamfanin, bisa tanadin yarjejeniyar ci gaban al’umma (CDA). Wannan faɗaɗawar da aka yi da gangan na nuni da burinmu na tabbatar da adalci, haɗin kai da raba riba daidai a tsakanin al’ummominmu.”
“Dangote Cement Plc na ci gaba da aiwatar da wannan shirin tallafin ilimi tsawon shekaru, kuma zai ci gaba da haka, domin muna da yakinin cewa idan al’ummominmu suka bunƙasa, harkokin kasuwancinmu ma za su bunƙasa. Shirye shiryen CSR ɗinmu ba kyauta ne kawai na lokaci ɗaya ba, amma zuba jari ne na dogon lokaci domin samar da tasiri mai ɗorewa.”
“Yayin da muke taya masu cin gajiyar murna, muna ƙarfafa su da su yi amfani da kuɗin tallafin cikin hikima da gaskiya domin dalilan karatu.
Ana gudanar da tsarin tallafin cikin gaskiya da adalci ta hanyar kwamitin da kamfanin ya kafa domin tabbatar da adalci a tsakanin dukkan al’ummomin da ke amfana.”
“Baya ga tallafin karatu, Dangote Cement Plc na da ƙwarin gwiwa wajen inganta rayuwar al’umma da walwala a cikin al’ummomin da ke karɓar bakuncinsa.
Tare da haɗin gwiwar shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki, muna ci gaba da ƙirƙira da aiwatar da shirye shiryen bisa tanadin CDA da manufar CSR ɗinmu.”
“A shekarar 2025, Reshen Gboko ya ƙaddamar da shirye shiryen ci gaban al’umma da suka haɗa da: Shirin Ƙarfafa Mata 150, Shirin Ƙarfafa Manoma, mutane 50, da Shirin Ƙarfafa Matasa 30, da sauran shirye shirye masu amfani.”
“Al’ummomin da suka amfana da waɗannan shirye shiryen sun haɗa da: Tse-Kucha, Quarry, Amua, Mbazembe, Mbatur, da Pass Brothers.”
“Bikin yau ya kuma nuna kammala Shirin Ƙarfafa Matasa, inda aka raba takardun shaidar kammala horo da kayan fara sana’a ga mahalarta.”
“Waɗannan shirye shiryen an tsara su ne ba kawai don koyar da sana’a ba, amma don dawo da mutunci, ƙarfafa dogaro da kai, da kuma samar da hanyoyin rayuwa masu ɗorewa a cikin al’umma.”
Sarkin Gboko, Ter Gboko, Gabriel Shosum, ya shawarci duk masu cin gajiyar da su yi amfani da tallafin cikin hikima. Mue Ter Gboko, Ikpa Ahua, ne ya wakilce shi.
Wakiliyar Hukumar Horas da Masana’antu (ITF), Mrs. Sarah Adeniyi, ta bayyana Dangote Cement Plc a matsayin abokin haɗin gwiwa na kwarai duba da goyon bayan da yake bayarwa wajen ci gaban matasa.
Wani ɗalibi mai shekaru 16 da ya amfana, kuma ɗalibi a makarantar Amua Memorial Grammar School, Gabriel Yo Hol, ya gode wa kamfanin bisa tallafin karatu tare da alƙawarin zama jakadan Dangote Cement Plc.














