Daga Bashir Bello
A wani bangare na kokarin bunkasa ababen more rayuwa na makamashi a Najeriya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC Ltd) ya sanar da kammala gyaran bututun Escravos Lagos Pipeline System (ELPS) gaba daya, bayan wani gaggawan martani da aka dauka kan fashewar da ta faru a ranar 10 ga Disamba, 2025.
Bututun ELPS, wanda ke da matukar muhimmanci wajen isar da iskar gas daga yankin Niger Delta mai arzikin mai zuwa Lagos da sauran sassan kudu maso yammacin Najeriya, ya samu tsaiko sakamakon fashewar da ba a zata ba a kusa da Garin Warri.
A matsayin martani, NNPC Ltd ta hanzarta aiwatar da matakan gaggawa, inda ta tura kwararrun kungiyoyi daga fannoni daban daban domin dakile lamarin da kuma fara aikin gyara.
A cewar wata sanarwa da Andy Odeh, Babban Jami’in Hulda da Jama’a na NNPC Ltd ya fitar, an gyara sashen da ya lalace, an gwada shi da matsin lamba, sannan aka dawo da shi aiki cikin kankanin lokaci.
“Yau, bututun ya dawo aiki gaba daya, abin da ke nuna juriyarmu da kuma jajircewarmu wajen tabbatar da tsaron makamashi,” in ji sanarwar.
An samu nasarar wannan gyara ne sakamakon hadin gwiwar da aka samu daga al’ummomin da ke karbar bakuncin bututun, hukumomin da ke sa ido, jami’an tsaro da kuma abokan hulda na fasaha. NNPC Ltd ta yaba da wannan hadin gwiwa a matsayin abin koyi wajen tafiyar da rikici da kuma dorewar ababen more rayuwa.
“Mun mayar da wannan lokaci mai wahala zuwa labarin nasara, inda muka dawo da ayyuka cikin lokaci tare da kiyaye mafi ingancin matakan tsaro da kula da muhalli,” in ji Odeh.
Bututun Escravos Lagos wani ginshiki ne na hanyar rarraba iskar gas a cikin gida a Najeriya, wanda ke ciyar da tashoshin wutar lantarki, masana’antu da cibiyoyin rarraba makamashi a fadin kasar. Dawowar sa aiki cikin gaggawa ana sa ran zai daidaita isar da iskar gas da kuma tallafa wa harkokin tattalin arziki, musamman a bangaren wutar lantarki da masana’antu.
NNPC Ltd ta sake jaddada kudurinta na kare muhalli, tabbatar da tsaron al’umma da kuma kiyaye ingancin kadarorinta na kasa.
“Yayin da muke ci gaba, NNPC Ltd na nan daram da alkawarin kare muhalli, kare al’umma da kuma tabbatar da inganci da amincin kadarorinmu,” in ji sanarwar.
Martanin gaggawa da nasarar da aka samu wajen dawo da bututun ELPS ya kara jaddada sabon matsayi da kamfanin ke dauka a matsayin kamfani na kasa da ke tafiya da tsarin kasuwanci, mai mayar da hankali kan inganci da amincewar masu ruwa da tsaki.
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke kara zage damtse wajen karfafa ababen more rayuwa na makamashi da kuma tabbatar da isar da makamashi ba tare da tangarda ba domin biyan bukatun cikin gida da na masana’antu da ke karuwa.
Yanzu da bututun ELPS ya dawo aiki, masu ruwa da tsaki na cike da fata kan ingantacciyar isar da makamashi da kuma daidaiton tattalin arziki a watanni masu zuwa.



















