Daga Ahmed Aliyu
Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekara hamsin da biyar 55.
Gwamna Radda ya bayyana Gwamna Uba Sani a matsayin “jagora mai sauya al’amura da kuma dan dimokuradiyya na hakika wanda tafiyarsa daga gwagwarmayar kare hakkin dan Adam zuwa shugabancin zartarwa ke ci gaba da zaburar da sabbin matasan Najeriya.”
Hakkan na kunshe ne a wata Sanarwa dauke da sa hannun Mallam Ibrahim Kaula Mohammed,
Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Katsina.
Ya lura cewa Gwamna Uba Sani ya kasance mai nuna jarumta, hangen nesa, da kishin kasa a cikin hidimarsa ga Najeriya.
A cewar Gwamna Radda, asalin Gwamna Uba Sani a matsayin “injiniyan injina, mai fafutukar kare hakkin dan Adam, ma’aikacin ci gaba, da kuma gogaggen dan majalisa ya taimaka matuka wajen gina salon mulkinsa mai ma’ana da kuma mai mayar da hankali kan bukatun jama’a.”
Ya kara da cewa “wadannan gagarumin kwarewa sun kara karfafa jajircewarsa wajen gaskiya da rikon amana, hadin kai, da kuma kula da jin dadin talakawa.”
Gwamna Radda ya yaba da sadaukarwar Gwamna Uba Sani wajen ci gaban da ya hada kowa da kowa da kuma tsarin zaman lafiya na Kaduna, wanda ya karfafa hadin kai a cikin al’umma da kuma zurfafa amincewar jama’a da dimokuradiyya.
Ya bayyana cewa “salon jagorancinsa mai natsuwa da kuma gina zaman lafiya ta hanyar tattaunawa sun taimaka wajen karfafa hadin kai tsakanin al’ummomi daban daban a Jihar Kaduna.”
Haka kuma, ya jaddada irin gagarumar gudunmawar Gwamna Uba Sani a Majalisar Dattawa, inda ya tuna da lokacin da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a matsayin Sanata, inda ya shugabanci Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Banki, Inshora da Sauran Harkokin Kudi, tare da jagorantar muhimman sauye sauyen tattalin arziki da suka amfani kasa.
Gwamna Radda ya kara yabawa da yadda ya cika alkawuransa ta hanyar manyan ayyuka a fannonin ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma, da ilimi, yana cewa: “Ayyukansa na gina hanyoyi, gyaran asibitoci, tallafin noma, da sauye-sauyen ilimi shaida ne na jagoranci mai nasara.”
Ya bayyana Gwamna Uba Sani a matsayin “mai hada kan jama’a daga jam’iyyu da yankuna daban-daban, wanda jajircewarsa ga zaman lafiya, tsaro, da hadin gwiwar tattalin arziki ke kara karfafa Arewa maso Yamma da Najeriya baki daya.”
Ya kuma yaba da sadaukarwar Gwamna Uba Sani ga dimokuradiyya da kare hakkin dan Adam tun daga shekarun farko na gwagwarmayarsa.
A madadin Gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina, Gwamna Radda ya taya Sanata Uba Sani murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekara ta 55, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kara masa lafiya, hikima, da karfi domin ci gaba da yi wa Jihar Kaduna da Tarayyar Najeriya hidima mai ma’ana.



















