Yayin da muka shiga sabuwar shekara cike da sabuwar fata na hadin gwiwa, ina mika gaisuwa ta musamman ga al’ummar Najeriya musamman Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da abokanmu a fadin Afirka da duniya baki daya.
Sabuwar shekara dama ce ta musamman da za ta ba mu zarafin sabunta kudurinmu na bin dabi’un da ba su da iyaka kamar mutunci, adalci, zaman lafiya da girmama juna. A wannan lokaci da al’ummominmu ke fuskantar kalubale masu sarkakiya, wajibi ne mu tashi tsaye da hadin kai da manufa guda ta hanyar karfafa hukumomi, kare masu rauni, da karfafa tattaunawa maimakon rarrabuwar kawuna.
A matsayina na Shugaban Kwamitin Shawara na Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (Nigeria) da kuma Mashawarcin Musamman kan Harkokin Gwamnati a Nahiyar Afirka, ina sake jaddada cikakken kudurina na kare hakkin dan Adam, inganta shugabanci na kowa da kowa, da kuma ci gaba mai dorewa a nahiyarmu.
Tare, za mu iya gina al’umma inda adalci ke da tushe, dama ke daidai, kuma doka ke kare kowa da kowa.
Allah ya sanya wannan sabuwar shekara ta zamo abin da zai motsa mu mu yi aiki da tausayi, jarumtaka da gaskiya. Mu hada kai gwamnatoci, kungiyoyin fararen hula da yan kasa gaba daya don gina makoma mai cike da zaman lafiya, arziki da mutunta juna.
Ina yi muku fatan lafiya, ci gaba da nasara mai dorewa a wannan sabuwar shekara.
Barka da Sabuwar Shekara
Mai Girma Jakada Dr. Malami Shehu Ma’aji (MFR) Shugaban Kwamitin Shawara, Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (Nigeria)
Mashawarci na Musamman kan Harkokin Gwamnati a Nahiyar Afirka



















