Daga Bashir Bello, Abuja.
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta nada babban jigo a siyasa kuma tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna a matsayin ɗan kwamitin sake duba kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Wannan naɗin ya fito ne a cikin wata wasiƙa a ranar 8 ga Janairu, 2026, wadda shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata David Mark ya sanya hannu.
Wasiƙar ta bayyana zaɓen Farfesa Bello a matsayin ɗan Kwamitin Sake Duba Kundin Tsarin Mulkin ADC; matsayi mai daraja da aka tanadar ga mutanen da ke da cikakkiyar gaskiya da fahimtar mulkin dimokuraɗiyya sosai.
Manufar kwamitin ta kasance a bayyane: duba tsarin kundin mulkin jam’iyyar na yanzu, bayar da shawarwari kan gyare-gyare, tare da tabbatar da cewa tsarin jam’iyyar ya tsaya kan ka’idojin gaskiya, bin doka da oda, da dimokuraɗiyyar cikin gida.
Yayin da tsarin siyasar Najeriya ke ci gaba da sauyawa cikin sauri, ADC ta nemi daidaita kundinta da manufofin asali da kuma mafi kyawun ƙa’idojin dimokuraɗiyya na zamani.
“Zamaninka a cikin kwamitin zai fara aiki daga ranar 8 ga Janairu, 2026,” in ji wasiƙar.
Wannan naɗin zai ba shi damar bayar da gudummawar muryarsa da basirarsa wajen gina ƙungiyar siyasa mai haɗa kan jama’a da kuma inganci.
Za a iya tunawa cewa Farfesa Bello ya ajiye mukaminsa na Kwamishina kuma ɗan Majalisar Zartarwa ta Jihar Kaduna a watan Yuli bara. Sai dai ya ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar APC mai mulki har sai da ya janye ya koma jam’iyyar haɗin gwiwa ADC a ranar 7 ga Janairu, 2026.
A wurin ADC, naɗin Farfesa Bello ya nuna jajircewa wajen jagoranci mai ma’ana da kuma sake tabbatar da burinta na gina tsarin siyasa da zai yi wa jama’a hidima tare da ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya daga ciki. A wurin Farfesa Bello, wanda ya dade a harkar ilimi kuma mai fafutukar gyaran cibiyoyi, wannan naɗin ba kawai girmamawa ba ne; kira ne zuwa hidima.





















