Daga Bashir Bello
Kamfanin Man Fetur na Dangote ya sanar da fara sayar da fetur mai inganci da aka tace a cikin gida a farashin Naira 739 kowace lita a dukkanin tashoshin MRS da ke fadin Najeriya.
A cewar Sanarwan, akwai sama da tashoshi 2,000 na MRS da ke aiki a halin yanzu, da karin wasu da za su shiga nan ba da jimawa ba, direbobi da masu ababen hawa za su iya samun fetur mai araha da inganci a kowane yanki na kasar.
Sanarwan ya Kara da cewa, Wannan mataki wani bangare ne na kudurin Dangote na tabbatar da yancin makamashi da kuma yaki da tsadar farashin fetur da ake yi wa yan kasa.
Kamfanin yana kira ga jama’a da Kada su amince da tsada fiye da kima, tare da tabbatar da cewa ba za a biya fiye da Naira 739 kowace lita ba.
Har ila yau, Sanarwan ya ce, Idan wani tashar MRS na sayar da fetur fiye da wannan farashi, ana bukatar a kai rahoto ta wannan lambar 0800 123 5264.
Kamfanin Man Fetur na Dangote na ci gaba da jajircewa wajen samar da makamashi mai araha da dogaro da kai ga daukacin yan Najeriya.



















