Kamfanin Dangote Cement Plc ta Ibese Plant dake Jihar Ogun ta kaddamar da wani shiri mai suna Safety FairPlay Initiative domin inganta sauyin dabi’u da al’adu wajen bin ka’idojin tsaro a tsakanin ma’aikatanta.
An shirya aiwatar da wannan shiri a dukkanin sauran wuraren kamfanin Dangote Cement Plc, wanda ya zama babban mataki wajen ƙarfafa al’adar tsaro a kamfanin. Kaddamar da shirin a matakin farko ya samu halartar shugabanni da ma’aikata da dama, wanda ya nuna haɗin gwiwar kowa wajen tabbatar da tsaro a wurin aiki.
Shirin Safety FairPlay Initiative an tsara shi ne domin samar da sauyin dabi’u da al’adu na dindindin ta hanyar tsarin adalci da gaskiya wanda ke ƙarfafa bin ka’idojin tsaro. An gina shi a kan ginshiƙai uku: Girmamawa, Gyara (Coaching), da Ladabtarwa. Shirin yana ba da lada ga kyakkyawan ɗabi’ar tsaro, yana tabbatar da daidaito wajen magance ayyukan da ke da haɗari, tare da ƙarfafa bayar da rahoton abubuwan da suka faru, kuskure ko kusantar hatsari.
A yayin kaddamarwa, Daraktan Fasaha na DCP, Mista Anandam Duraisamy, ya jaddada muhimmancin shirin ga harkokin kasuwanci, tare da kira ga ma’aikata su rungumi al’adar tsaro bisa adalci, ɗaukar alhaki, girmamawa da ci gaba da ingantawa.
Duraisamy ya bayyana cewa Safety FairPlay wata shiri ce ta sauyi a tafiyar kamfanin wajen gina wurin aiki da tsaro ba kawai a matsayin doka ba, amma a matsayin tunani da dabi’a ta kullum wacce ke bayyana mu da yadda muke aiki.
“Mun zo ne domin kaddamar da shiri da zai sauya ba kawai abin da muke yi ba, har ma yadda muke tunani, yadda muke aikatawa da yadda muke mayar da martani dangane da tsaro.”
Ya ce: “Safety FairPlay yana nufin gina amana, daidaito da ɗaukar alhaki wajen kula da tsaro. Idan mutane sun san cewa ana yaba kyakkyawan ɗabi’a, ana magance haɗari cikin adalci, kuma ana ɗaukar kowa daidai, tsaro zai zama alhakin kowa kuma wani ɓangare na al’adarmu.”
Shirin ya shafi sauyin dabi’u da al’adu. Yana gane cewa cikakken tsaro ba ya tsaya ga kayan aiki, tsari ko bin doka kawai; yana farawa ne daga mutane dabi’unmu, zaɓinmu, da shirinmu na kula da juna.
Duk wani hatsari da aka hana, duk wani haɗari da aka gano, da duk wani aikin tsaro da aka yi yana ƙarfafa ƙungiyarmu. Wannan ƙarfi yana fitowa daga ku daga kowanne ɗan ma’aikata da ya rungumi tsaro a matsayin alhakin kansa da kuma ƙima ta haɗin gwiwa.
Shi ma Shugaban Sashen Lafiya, Tsaro da Muhalli (HSE) na Ibese Plant, Mista Elvis Akalusi, ya yaba wa shugabancin DCP bisa jagorantar shirin tare da jinjinawa ma’aikata bisa yadda suka rungumi shirin da farin ciki.
Ya tabbatar da cewa Safety FairPlay Initiative za ta kasance cikakkiyar ɓangare na ayyukan yau da kullum a Ibese Plant tare da haɗin gwiwar dukkan shugabannin sassa. Ya ce: “Wannan shiri zai samar da kayan aiki, horo, girmamawa da ɗaukar alhaki da ake buƙata domin taimaka mana mu yanke shawara mai tsaro. Amma nasarar shirin tana dogara ne da haɗin gwiwarmu da ƙarfin gwiwarmu na yin abin da ya dace koyaushe, ko da babu wanda ke kallonmu.”
“Mu shiga wannan sabon babi da buɗaɗɗen zuciya da ƙudurin ingantawa. Mu gina al’ada inda a kan ƙarfafa magana, koyon sabbin abubuwa ya zama na dindindin, kuma kuskure ya zama dama ta ci gaba ba dalilin tsoro ba.”
Da kaddamar da Safety FairPlay, Dangote Cement Ibese Plant ta ƙara tabbatar da matsayinta a matsayin kamfani mai mayar da hankali kan tsaro, mai kishin kare ma’aikatansa, dukiyoyinsa da kuma dorewar ci gabansa.





















