Daga Bashir Bello
Alhaji Aliko Dangote, Shugaban Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, ya sanar da wani shirin tallafin karatu na Naira Tiriliyan Daya domin fadada damar samun ilimi da kuma karfafa hazaka a fadin Najeriya.
Wannan shiri zai fara aiki daga shekarar 2026, inda za a tallafa wa dalibai sama da miliyan 1.3 daga kananan hukumomi 774 na kasar, tare da ware Naira Biliyan 100 a kowace shekara na tsawon shekaru goma.
Shirin ya mayar da hankali ne kan daliban da suka fi bukata a Najeriya, kuma an raba shi zuwa rukuni uku:
Aliko Dangote STEM Scholars, Dalibai 30,000 a jami’o’in gwamnati da kwalejojin kimiyya za su samu tallafin karatun har zuwa Naira 600,000 a kowace shekara.
Aliko Dangote Technical Scholars, Matasa 5,000 masu koyon sana’o’in fasaha za su samu kayan karatu da na aikin hannu.
MHF Dangote Secondary School Girls Scholars, Yan mata 10,000 a makarantun sakandare na gwamnati za su samu kayan makaranta, littattafai da kayan koyarwa, musamman a jihohin da ke da yawan yara mata da ba sa zuwa makaranta.
Za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar hukumomin NELFUND, JAMB, NIMC, NUC, NBTE, WAEC da NECO, ta hanyar tsarin tantancewa da rabon tallafi na zamani da ya dogara da cancanta.
Dangote ya bayyana cewa wannan wani muhimmin jari ne a bangaren ci gaban dan Adam, wanda zai rage gibin da ke tsakanin masu hali da marasa hali, tare da bunkasa ci gaban kasa.
An kafa kwamitin jagoranci na shirin karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Lafia, Mai Shari’a Sidi Dauda Bage. Dangote ya sha alwashin ware kashi 25 cikin 100 na dukiyarsa domin dorewar shirin, wanda za a duba ci gaban sa a cikin tsarin hangen nesa na Dangote Group na shekarar 2030.
Dangote ya ce daliban da suka fi bukata ne za su fi amfana da wannan shiri, yana mai jaddada cewa rashin kudi ne ke hana yawancin matasa ci gaba da karatu, ba rashin basira ba. Ya ce wannan ba sadaka ba ce kawai, illa wani zuba jari ne mai zurfi a makomar Najeriya.
“Kowane yaro da muka taimaka ya ci gaba da karatu yana karfafa tattalin arzikinmu. Kowane dalibi da muka tallafa yana rage bambanci. Kowane mai karatu da muka karfafa zai zama ginshikin ci gaban kasa a nan gaba,” in ji shi.
Dangote ya kara da cewa Gidauniyar ADF ta dade tana mayar da hankali kan lafiya da abinci a matsayin ginshikan ci gaban dan Adam, amma halin tattalin arzikin yanzu ya sanya tallafin ilimi ya zama dole.
Ya ce: “Babu dalilin da zai sa matashi ya daina karatu saboda rashin kudi. Muna daukar mataki domin tabbatar da cewa dalibai sun ci gaba da karatu da cimma burinsu. Wannan shiri ya wuce tallafin kudi kawai, zuba jari ne a jikin dan Adam, wanda zai haifar da tasiri mai fadi a tattalin arziki, al’umma da kuma al’ummomi masu zuwa.”
Ya bayyana ilimi a matsayin “tushen kowace al’umma mai ci gaba,” yana mai cewa ilimi shi ne mafi karfi wajen daidaita bambance bambance da kuma bunkasa rayuwar jama’a. Duk da haka, ya gargadi cewa dalibai masu hazaka da dama a Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da ke barazana ga ci gaban su. “Ba za mu yarda da talauci ya hana matasanmu cika burinsu ba musamman idan makomar kasar nan na dogara da basirar su, juriya da shugabancinsu,” in ji shi.
Shirin zai mayar da hankali kan sakamako mai auna tasiri kamar ci gaba da halartar makaranta, kammala karatu da tasirin bayan makaranta. Dangote ya ce burin wannan shiri shi ne bai wa kowane yaro mai cancanta damar karatu ba tare da shinge na kudi ba, tare da ‘yancin mafarki da kayan cimma nasara.
Mambobin kwamitin jagoranci sun hada da tsofaffin shugabannin jami’o’i, manyan jami’an ilimi, kwararru da wakilan dangin Dangote.
A jawabinsa, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da hangen nesa da gudummawar Dangote ga ci gaban kasa, yana mai cewa wannan shiri ya nuna muhimmancin hadin gwiwar masu zaman kansu a ci gaban kasa.
Ya ce yawan jama’a a Najeriya na bukatar zuba jari cikin gaggawa a fannin ilimi, domin al’umma ba za ta ci gaba ba idan ba ta da ilimi.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana shirin a matsayin “cikakken ci gaban dan Adam,” yana mai cewa yana da daidaito da tsarin gwamnatin Tinubu na sauya Najeriya daga tattalin arzikin da ya dogara da albarkatu zuwa wanda ya dogara da ilimi.
Shima a jawabinsa, Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ya wakilci sauran gwamnoni 36 wajen yabawa da kuma alkawarin goyon bayan su ga shirin.
Mai Martaba Sarkin Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya bayyana wannan shiri a matsayin wani babban sauyi da kuma zuba jari mai ma’ana a makomar Najeriya, yana mai tuna yadda Gidauniyar ADF ta taimaka wa al’ummarsa a lokacin rikicin kabilanci.
A cikin jawabin ta daga Amurka, Mataimakiyar Sakataren Gwamnatin Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta ce wannan shiri zai samar da yanayi mai kyau ga yara su koyi ilimi da kuma taimaka wa iyalai su samu ci gaba.



















