Daga Bashir Bello
Wani fashewar bututun gas da ake zargin ya faru a kan bututun iskar gas na Escravos zuwa Lagos da misalin karfe 5:50 na yamma a ranar Talata, goma (10 ) ga Disamba, 2025, a kusa da kauyukan Tebijor, Okpele, da Ikpopo a masarautar Gbaramatu da ke Jihar Delta, ya sa Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC Ltd.) daukar matakan gaggawa cikin hanzari.
A wata sanarwa da Babban Jami’in Hulda da Jama’a na NNPC Ltd., Mista Andy Odeh, ya fitar a ranar Laraba, 11 ga Disamba, kamfanin ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa binciken farko ya nuna raguwar matsin lamba a bututun da abin ya shafa alamar cewa an samu fitar iskar gas daga bututun mallakar Kamfanin Kula da Bututun Gas na NNPC (NGIC). Sai dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin fashewar ba, har sai an kammala cikakken bincike.
“Abin da yafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne kare lafiyar al’ummomin da ke kusa da wurin da kuma kare muhalli,” in ji sanarwar.
NNPC Ltd. ta bayyana cewa ta hanzarta aiwatar da matakan gaggawa da zarar lamarin ya faru. Kamfanin yana aiki tare da hukumomin gwamnati, jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin tabbatar da hadin gwiwa wajen rage illar fashewar.
Duk da cewa ba a tantance girman barnar ba tukuna, kamfanin ya tabbatar wa jama’a cewa yana da cikakken kudiri na kiyaye ka’idojin tsaro da kare muhalli.
“Muna aiki tukuru domin gano musabbabin fashewar. Ana gudanar da cikakken bincike, kuma za a ci gaba da sanar da jama’a da zarar an samu karin bayani,” in ji Mista Odeh.
Bututun Escravos zuwa Lagos na daya daga cikin muhimman hanyoyin rarraba iskar gas a Najeriya, wanda ke kai iskar daga yankin Niger Delta zuwa sassa daban daban na kasar, ciki har da Lagos da sauran jihohin kudu maso yamma. Duk wata tangarda a ayyukansa na iya shafar samar da wutar lantarki da kuma masana’antu.
Sanarwan ta bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu yayin da hukumomi ke ci gaba da sa ido da daukar matakan tsaro.
Wannan lamari ya kara jefa damuwa kan tsaron bututun mai da gas a Najeriya, musamman a yankin Niger Delta da ke fama da matsalolin fashewar bututu da lalacewar muhalli tun tsawon lokaci.
Za a ci gaba da kawo rahotanni yayin da karin bayani ke fitowa.



















