Daga Bashir Bello
Gwamna Malam Umar Namadi na Jihar Jigawa ya amince da nadin jami’ai 27 na cibiyoyin kananan hukumomi domin aiki a karkashin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa a shirin gudanar da aikin Hajjin 2026.
Sanarwar nadin jami’an ta fito ne daga hannun Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Habibu Yusuf Babura.
An sanar da amincewar ne a ranar 30 ga Disamba, 2025, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen da ake ci gaba da yi domin tabbatar da ingantaccen shiri da daidaitaccen tafiyar da aikin Hajji ga masu niyyar zuwa daga jihar.
Wannan ci gaba mai kyau ana sa ran zai kara karfin aiki na Hukumar Jin Dadin Alhazai da kuma inganta ayyukan da za a gudanar yayin aikin Hajjin 2026 a Saudiyya.
Yayin da yake mayar da martani kan wannan ci gaba, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya taya sabbin jami’an da aka nada murna tare da bukatar su gudanar da aikinsu da sadaukarwa da kwarewa.
Ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na Jihar Jigawa da Najeriya baki daya a duk tsawon aikin Hajjin.
Darakta Janar din ya kuma yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon bayan da yake ci gaba da bayarwa ga alhazan jihar, yana mai cewa wannan mataki zai taimaka matuka wajen samun nasarar aikin Hajjin 2026 daga jihar da kuma kasa baki daya.

















