Daga Bashir Bello
Majalisar Dattawan Najeriya ta nuna damuwa matuƙa kan ayyukan sojojin Amurka da aka gudanar a cikin ƙasar nan.
Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar Bauchi Central Senatorial District, ya soki harin da sojojin Amurka suka kai kan sansanonin ‘yan ta’adda da ‘yan fashi, yana mai cewa an gudanar da wannan aiki ba tare da amincewar Majalisar Dattawa ba.
Yayin zaman majalisa ta hanyar oda na gata, Sanata Ningi ya jaddada cewa wannan aiki ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya kuma ya karya yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.
Ya yi nuni da cewa irin waɗannan ayyuka na son rai suna tauye ‘yancin Najeriya da cikakkiyar ikon mallakar ƙasa.
Yayin da yake magana da ‘yan jarida bayan zaman majalisar, ɗan majalisar ya bayyana cewa ba a tattauna wannan batu a cikin zauren majalisa ba saboda bai shiga cikin dokokin zaman majalisar ba.
Ya Kara da cewa ko shugaban ƙasa ma ba shi da ikon ba wa ƙasashen waje damar kai hare-hare na soja ba tare da amincewar majalisar ba.
“A matsayimmu na wakilan jama’a, kundin tsarin mulki ya ba mu ikon amincewa da irin waɗannan ayyuka,” in ji Ningi.
Sanatan, wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda ya taɓa fuskantar ta’addanci kai tsaye, ya tuna cewa marigayi kawunsa, tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Boko Haram suka kashe shi a gonarsa.
Ya sake jaddada goyon bayansa ga kawar da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi, amma ya nace cewa duk wata haɗin gwiwa da ƙasashen waje dole ne ta samu sahalewar Majalisar Ɗinkin Najeriya domin tabbatar da inganci.
Sanata Ningi ya kuma yi gargadin cewa barin irin waɗannan ayyuka su ci gaba na iya ƙarfafa wasu manyan ƙasashe su tauye ikon mallakar Najeriya har ma su yi garkuwa da shugabannin ƙasa, yana kawo misali da yadda Amurka ta yi a kasar Venezuela.





















