Daga Bashir Bello
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin kungiyoyin likitocin jihohi a dakin taro na Hajj House da ke Abuja.
Farfesa Usman ya bayyana cewa manufar taron ita ce fara shirye shiryen aikin likitanci na Hajjin 2026 cikin tsari, 6tare da tabbatar da cewa an daidaita da dokokin kiwon lafiya da Masarautar Saudiyya ta fitar, wadanda ya bayyana a matsayin dole ne kuma ba za a iya sassauta su ba.
Ya jaddada cewa bayar da kulawar lafiya yayin aikin Hajji babban nauyi ne da ke bukatar shiri tun da wuri, daidaituwa mai kyau da kuma bin ka’idoji yadda ya kamata domin kare lafiyar alhazan Najeriya.
Shugaban NAHCON ya bayyana cewa a matsayinta na hukumar da ke da alhakin kula da harkokin aikin Hajji a Najeriya, hukumar na da niyyar tabbatar da cewa ayyukan kiwon lafiya da ake bayarwa ga alhazai sun dace da ka’idojin kasa da kasa da na Saudiyya, ta hanyar ladabi, kwarewa da hadin gwiwa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki.
Ya tabbatar wa kungiyoyin likitocin jihohi da cikakken goyon bayan NAHCON, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da bayar da jagoranci, daidaitawa da sa ido domin karfafa shirin kiwon lafiya kafin aikin Hajjin 2026.
Farfesa Usman ya jaddada cewa ba za a bar wani bangare na kiwon lafiyar alhazai ga sa’a ba, yayin da Najeriya ke kokarin tabbatar da ingantacciyar da kuma amintacciyar kulawar lafiya ga alhazanta a lokacin aikin Hajji.

















