

Kamfanin Dangote Cement Plc, reshen Gboko, ya kaddamar da wani cikakken shirin tallafin al’umma da nufin karfafa tattalin arziki mai dorewa a cikin al’ummomin da ke karbar bakuncin kamfanin.
Da yake jawabi a ranar Litinin a wani biki da aka gudanar a Gboko, Shugaban Sashen Ayyukan Al’umma na Dangote Cement Plc, Gboko Plant, Dr. Johnson Kor, ya bayyana cewa an tsara wadannan shirye shirye ne bisa yarjejeniyar ci gaban al’umma (CDA) da aka cimma tsakanin kamfanin da al’ummomin da ke karbar bakuncinsa.
“A watan Disamba na shekarar 2024, Dangote Group ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ci gaban al’umma (CDA) da al’ummomi shida da ke da hakkin hakar ma’adinai, ciki har da al’ummar Mbayion wacce ita ce babbar al’umma mai karbar bakuncin kamfanin. An tsara aiwatar da ayyuka da dama a cikin shekaru biyar,” in ji shi.
Ya bayyana cewa kamfanin ya riga ya kammala wasu ayyuka, yayin da wasu ke ci gaba da gudana, ciki har da Shirin Tallafa wa Mata, Shirin Tallafa wa Manoma, da Shirin Tallafa wa Matasa dukkansu da nufin inganta rayuwar al’ummomin da ke karbar bakuncin kamfanin.
A ranar Litinin, kamfanin ya mika takardun shaidar kammala karatu da kayan fara sana’a ga matasa 30 da suka kammala horo a cikin Shirin Raya Fasahar Matasa, domin su fara amfani da kwarewar da suka samu nan take kuma su dogara da kansu.
Sauran ayyukan da aka kammala sun hada da bude rijiyoyin burtsatse masu amfani da injin a unguwannin Mbaswa, Agboghol, Mbatyu da Pass Brothers.
Shima da yake jawabi, Daraktan Kamfanin DCP Gboko, wanda Babban Manajan Kudi, Olusegun Orebanjo, ya wakilta, ya ce: “A Dangote Cement Plc, ba ma kallon al’ummomin da ke karbar bakuncinmu a matsayin makwabta kawai, sai dai a matsayin abokan tafiya masu daraja.”
“Zamowarmu a Gboko na ginu ne bisa imani mai karfi cewa nasarar kasuwanci dole ne ta tafi da walwalar al’umma, kuma wannan manufa ce ke ci gaba da jagorantar ayyukanmu da zuba jari a al’umma. Wannan taron na yau shaida ne na wannan tafiya tare.”
Daraktan ya kara da cewa: “Muna tabbatar wa da duk masu ruwa da tsaki cewa ayyuka da dama da ke karkashin yarjejeniyar CDA na ci gaba da gudana cikin nasara. Duk da cewa wasu ayyuka ba su fara ba saboda wasu matsalolin fasaha, muna aiki tukuru don magance su. Muna tabbatar muku cewa dukkan ayyukan da suka rage za a aiwatar da su a shekara mai zuwa, tare da sabbin shirye-shirye da za su kara zurfafa tasirinmu a cikin al’umma.”














