

– Rukunin Dangote Industries Limited, Babban Daraktan Gudanarwa na Sashen Kayayyakin Kaya da Rarrabawa, Abdu Dantata;
– Rukunin Dangote Industries Limited, Babban Daraktan Gudanarwa na Sashen Kasuwanci (Siminti da Abinci), Mariya Aliko Dangote;
– Shugaban Kwamitin Daraktoci na NASCON Allied Industries PLC, Olakunle Alake;
– Mrs. Aderemi Saka, Manajan Darakta na NASCON Allied Industries Plc;
– Shugaban Kamfani / Babban Darakta na Dangote Industries Limited, Aliko Dangote;
– Rukunin Dangote Industries Limited, Babban Daraktan Gudanarwa na Sashen Kasuwanci (Matatar Mai da Sinadarai), Fatima Aliko Dangote;
– NASCON Allied Industries Plc, Darakta mara zaman kansa, Toya Lawani;
– NASCON Allied Industries Plc, Darakta mara zaman kansa, Fatima Wali-Abdurrahman;
A wajen NASCON Allied Industries Plc Customers Dinner / Awards Night da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 12 ga Fabrairu, 2026.
An gudanar da bikin bayar da kyautar ne a taron 2025 Customers Dinner and Awards Night, inda manyan shugabanni suka halarta, ciki har da shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, da mataimakin shugaban kamfanin, Olakunle Alake.
NASCON Allied Industries Plc, reshen kamfanin Dangote Industries Limited, shi ne babban mai samar da gishiri da kayan dandano na Dangote Classic Seasonings a Najeriya.
A Jawabinsa, Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa wannan bikin karramawa na abokan ciniki yana nuna muhimmancin hidimar abokan ciniki a matsayin ginshiƙin kamfanin, tare da hangen nesa na zama kamfani mai inganci a duniya.
Ya kuma yaba da jajircewar shugabannin kamfanin da ma’aikata wajen tabbatar da ci gaba da jagoranci a kasuwa.
“Karrama abokan ciniki ba wai kawai kyakkyawan hulɗa ba ne, amma kasuwanci ne mai kyau” ya ce.
“Zamu ci gaba da saka hannun jari a ingancin alama, ingancin sarkar samarwa, dorewa, da fasahar zamani. Amma duk wannan ba zai yi tasiri ba sai idan ya dace da bukatun abokan ciniki.” Acewar sa.
Olakunle Alake, shugaban kwamitin NASCON, ya jaddada cewa hidimar abokan ciniki ba kawai ƙima ba ce, amma babban kayan aiki na dabarun kasuwanci.
Ya Kara Bayyana cewa bikin kyautar yana matsayin bikin haɗin gwiwa, inda ya ce nasara ba za ta samu ba tare da goyon bayan abokan ciniki.
Sabon daraktan gudanarwa na Matatar mai na Dangote Refinery and Petrochemicals Fatima Aliko Dangote, ta nuna godiya ga abokan ciniki bisa amincewa da kamfanin.
Ta ce: “Kowane ɗaya daga cikinku ya nuna jajircewa ta musamman wajen tallata kayayyakinmu. Nasarar ku tana da alaƙa kai tsaye da nasarar mu.”
Mariya Aliko Dangote, daraktar gudanarwa ta bangaren kasuwanci (Cement da Foods),
ta ce: “Nasara ta gaskiya tana fitowa daga kasuwa da kuma ra’ayin abokan ciniki. Wannan goyon bayan ku shi ne ginshiƙin ci gabanmu.”
Aderemi Saka, Manajan Darakta na NASCON, ya bayyana cewa babban saƙon taron shi ne nuna godiya da karramawa ga abokan ciniki, domin nasarar kamfanin tana da alaƙa da nasarar su.
Ali Balarabe ya gode wa kamfanin bisa kyautar motar taya 20 da kuɗi, a madadin waɗanda aka karrama yana mai alkawarin ci gaba da jajircewa da goyon baya.
Sauran waɗanda suka samu kyautar sun haɗa da: Alhaji Ibrahim Achida daga Muabsa Integrated Services sai Fanisau Enterprises da Idris Saleh Nigeria Limited Sauran sun hada da Sani Adamu Trader da GIA Global Concept.





















