Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, SAN, a ranar Laraba ya gabatar da adadin biliyan ₦184,392,160,433.00 a matsayin kasafin kuɗin da ma’aikatar ta tsara na shekarar 2026 ga kwamitocin Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan harkokin jiragen sama a Majalisar Dokoki.
Yayin gabatar da wannan tsarin Kasafin, Ministan ya nuna godiya ga kwamitocin bisa goyon baya da haɗin kai tun daga farkon wannan gwamnati. Ya jaddada kudirin ma’aikatar wajen ci gaba da kafa kyakkyawar alaƙa da Majalisar Dokoki domin haɓaka ci gaban masana’antar jiragen sama a Najeriya.
Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2026 an tsara shi ne ta yadda zai sabunta tsarin tsaro, inganta cibiyoyi da kuma ƙarfafa ci gaban ƙwarewar ma’aikata a fannin jiragen sama.
A cikin jawabin sa, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin jiragen sama, Sanata Buhari Abdulfatai, ya jaddada cewa dole ne a yi amfani da kuɗin jama’a cikin adalci, yana mai nanata cewa kundin tsarin mulki ya ba wa Majalisar Dokoki ikon ware kuɗi tare da tabbatar da gaskiya da bin doka.
Sanata Abdulfatai ya ƙara da ƙarfafawa Ministan da ya ci gaba da kyakkyawar alaƙa tsakanin ma’aikatar da kwamitin, tare da tabbatar da cewa kasafin kuɗin 2026 ya cimma manufofinsa.
Haka nan, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin jiragen sama, Rt. Hon. Abdullahi Idris, ya ba da shawarar cewa aiwatar da kasafin kuɗin ya kasance mai mayar da hankali ga al’umma, ya inganta ci gaban ababen more rayuwa, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasa.
Wainda Suka halarci Taron sun hada da Sakataren Dindindin na Ma’aikatar, Dr. Yakubu Adam Kofarmata, Daraktocin Ma’aikatar, da Shugabannin hukumomin da suka shafi Harkokin jiragen sama da dai sauran su.





















