





Daga Ahmed Aliyu
Gasar wasannin NNPC karo na 14 ta zo karshe cikin wani yanayi na farin ciki da murna a filin wasa na kasa Moshood Abiola da ke Abuja, inda Team Integrity daga yankunan Port Harcourt da Benin suka lashe kambin zakarun gasar bayan sun fi kowa yawan lambobin yabo.
Kungiyar Team Integrity ta samu lambobin zinariya 31, azurfa 18 da tagulla 21, tare da lashe kofuna tara, wanda hakan ya tabbatar da su a matsayin zakarun gasar.
Kungiyar Team Sustainability daga yankunan Abuja da Kaduna ta zo ta biyu da lambobin zinariya 15, azurfa 26 da tagulla 23, yayin da Kungiyar Team Excellence daga yankunan Legas da Warri ta zo ta uku da lambobin zinariya 13, azurfa 16 da tagulla 19.
A wata Sanarwa dauke da sa hannun Andy Odeh
Jami’in Hulda da Jama’a na NNPC Ltd. Ya ce A yayin bikin rufe gasar, Shugaban Kamfanin NNPC Ltd., Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana bajintar yan wasa a matsayin abin alfahari da ke nuna cewa kamfanin zai ci gaba da yin fice a fagen wasanni da kuma harkokin kasuwanci, ta hanyar jajircewa, hadin kai da kwarewa.
Ya kara da cewa NNPC Ltd na fatan kare kambinta a gasar wasannin masana’antar man fetur ta Najeriya (NOGIG) karo na 20 da za a gudanar a watan Fabrairun 2026, yana mai jaddada cewa yan wasan da suka fito daga wannan gasa za su ci gaba da daukaka sunan kamfanin.
“Ku ci gaba da nuna da’a kamar yadda kuka yi a wannan gasa; ku kara dankon zumunci da hadin kai; ku mai da kwarewar da kuka nuna a nan ta zama ginshikin ayyukanmu na yau da kullum,” in ji GCEO Ojulari.
A nata jawabin, Babbar Mataimakiyar Shugaban Kamfanin Mai Kula da Harkokin Kasuwanci, Sophia Mbakwe, ta ce daga abin da ta gani a gasar, “NNPC Ltd ba kawai za ta halarci gasar NOGIG mai zuwa ba, har ma za ta bar tarihi.”
Gasar ta bana mai taken “Energy In Motion: Compete, Connect & Celebrate” ta samu halartar yan wasa 450 daga sassa daban-daban na kamfanin, inda suka fafata a wasanni 13 da suka hada da kwallon kafa, kwallon kwando, kwallon raga, catur, 7k squash, scrabble, 8-ball pool, golf, tennis, tebur tennis, badminton, iyo da kuma gudu.
Baya ga nishadantarwa da karfafa zumunci, gasar ta zama wata hanya ta tantance yan wasa da za su wakilci NNPC Ltd a gasar NOGIG mai zuwa, inda kamfanin ke da tarihin lashe kambin zakara a kowace shekara.
A gasar NOGIG ta shekarar 2024 da aka gudanar a Abuja, NNPC Ltd ta lashe lambobin yabo 50, ciki har da zinariya 20, azurfa 9 da tagulla 21, wanda hakan ya tabbatar da ita a matsayin zakarar gasar.














