Shugaban kwamitin, Dan Majalisa Hon. Jafaru Mohammed, wanda ke wakiltar mazabar Agwara da Borgu a Jihar Neja, ya umarci sabon shugaban NAHCON da aka nada kwanan nan Ambassador Ismail Abba Yusuf da ya bayyana da kansa a gaban kwamitin ranar Talata, 24 ga Fabrairu, 2026.
Ya gargadi cewa rashin bayyana zai jawo hukunci mai tsanani daga Majalisar.
Wannan umarni ya biyo bayan matakin hukumar na tura wakili domin kare kasafin kudin shekarar 2026, abin da yan majalisar suka bayyana a matsayin raina majalisar.
“Tsoffin shugabannin hukumar sun saba kin bayyana da kansu. Wannan dabi’a ba za a sake yarda da ita ba”.
“NAHCON na da alhakin kula da harkokin Alhazai na Najeriya, kuma kwamitin na da hakkin sa ido bisa dokokin kasa.” Inji Hon. Jafaru.
Mambobin kwamitin ciki har da Hon. Shehu Ajilo sun nuna takaici kan abin da suka kira halin ko-in-kula na shugabancin NAHCON wajen amsa gayyatar majalisa.
Sun ce sauran hukumomi kan bayyana ba tare da wata matsala ba, amma NAHCON kullum kan kawo hujjoji marasa tushe.
“Wannan hali ba za a yarda da shi ba. Hukumar dole ta girmama majalisar wakilai.” Acewar Hon. Ajilo.
Kwamitin ya jaddada cewa shugabancin NAHCON dole ne ya nuna gaskiya da rikon amana, musamman kan harkokin da suka shafi jin dadin Alhazai na Najeriya. Idan ranar Talata ta zo, za a ga ko sabon shugaban zai bi umarnin.
Tsohon Shugaban Hukumar NAHCON professor Shehu Abdullahi ya Ajiye aikinsa a Yan kwanakin nan inda Shugaban Kada Bola Tinubu ya amince da Ambassador Ismail Abba Yusuf amatsayin Sabon Shugaban Hukumar.





















