Daga Bashir Bello
A Kokarin Kwamitin Wucin gadi na Majalisar Wakilai dake bincike Akan gyare gyaren da akayi a fannin Wutan lantarki na tsawon Shekaru sha bakwai, Majalisar ta ƙara zafafa bincikenta kan matsalolin da ke addabar bangaren wutar lantarki a Najeriya, inda take ci gaba kaddamar da bincike kan gyare-gyaren da aka yi tsakanin shekarar 2004 zuwa 2017.
Yan majalisar sun bayyana cewa duk da gagarumar zuba jari da gwamnatin tarayya ta yi da kuma shekaru da dama na bayar da tallafi, har yanzu miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da rashin wutar lantarki mai inganci.
Da yake jawabi a zaman sauraron bayani daga hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa (NERC) a gaban kwamitin binciken, shugaban kwamitin na wucin gadi, Hon. Ibrahim Al-Mustapha Aliyu, ya nuna damuwa matuka kan yadda bangaren ke ci gaba da fuskantar koma baya.
“Gwamnati ta zuba jari sosai tare da bayar da tallafi a fannin wutar lantarki, amma har yanzu ‘yan Najeriya na rokon samun wuta,” in ji Hon. Aliyu. “Lokacin yin shiru ya wuce.”
Kwamitin ya bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) ba su yi wani gagarumin zuba jari ba a cikin shekaru 14 da suka gabata, lamarin da ke haifar da tambayoyi kan jajircewarsu wajen inganta ayyuka.
Hon. Abubakar Hassan Fulata, daya daga cikin mambobin kwamitin, ya soki tsarin sayar da kamfanonin da kuma ci gaba da biyan su tallafi duk da rashin ingantaccen aiki.
“An biya biliyoyin naira a matsayin tallafi, amma babu wani abin a zo a gani,” in ji Fulata.
“An sayar da wadannan kamfanoni da farashi mai sauki. To, menene amfanin tallafin idan har ‘yan Najeriya ba su amfana da shi?”
A martaninsu, jami’an hukumar NERC sun kare kokarin da suke yi don inganta bangaren. Shugaban riko na hukumar, Yusuf Ali, tare da kwamishinan harkokin shari’a, Dafe Akpeneye, sun bayyana cewa tun daga shekarar 2018, an girka fiye da mita miliyan uku karkashin shirin Meter Asset Provider (MAP), wanda ya kai adadin masu mita zuwa miliyan bakwai daga cikin miliyan goma sha biyu da ke fadin kasar.
“Karkashin shirin MAP, yanzu muna da jimillar fiye da masu amfani miliyan bakwai da aka girka wa mita,” in ji su.
Duk da wadannan alkaluma, ‘yan majalisar sun jaddada cewa akwai bukatar kara zage damtse. Sun bukaci hadin gwiwa mai karfi tsakanin hukumomin gwamnati, masu sa ido da kuma masu zaman kansu domin tabbatar da cewa gyare-gyaren da aka yi a bangaren wutar lantarki sun haifar da sakamako mai gamsarwa ga ‘yan Najeriya.
Binciken dai na ci gaba, yayin da Majalisar Wakilai ke sha alwashin tabbatar da cewa an dauki matakin da ya dace kan duk masu ruwa da tsaki, tare da tura gyare-gyaren da za su sauya fasalin bangaren wutar lantarki a kasar.



















