Daga Ahmed Ahmed
Matatar Man Fetur ta Dangote ta fara sayar da Man Fetur (PMS) a fadin Najeriya a farashin ₦739 kowace lita a dukkan tashoshin mai na MRS Oil Nigeria Plc.
Wannan mataki na nuni da babban ci gaba a kokarin matatar wajen samar da mai, mai araha ga yan Najeriya da kuma daidaita kasuwar man fetur a kasa.
Akwai Sama da tashoshin MRS 2,000 a fadin kasa, ana sa ran sabon farashin zai fara aiki a dukkan wuraren, domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun amfana da wannan saukin farashi.
A cikin wata sanarwa, matatar ta yaba wa ‘yan kasuwa da suka rungumi sabon tsarin farashi, tare da bukatar sauran su bi sahu domin farfado da tattalin arzikin kasa.
“Muna yaba wa MRS da sauran ‘yan kasuwa da suka nuna kishin kasa ta hanyar saukar da farashin a matakin famfo. Muna kira ga sauran su shiga wannan yunkuri domin tallafa wa farfadowar tattalin arzikin Najeriya,” in ji matatar.
A tarihi, lokutan bukukuwa na da alaka da karancin mai da tashin farashi.
Sai dai Matatar Dangote ta kawo sauyi mai karfi a kasuwa ta hanyar rage farashin famfo a lokacin da yan Najeriya ke fuskantar kalubale. Tare da tabbacin samar da lita miliyan 50 a kowace rana, wannan shiri yana sauya tsarin samar da mai a lokacin bukukuwa.
Ta hanyar tace mai a cikin gida da yawa, matatar na rage dogaro da kasuwannin waje masu sauyin farashi, tana kare Najeriya daga Dogara Akan kudin waje, daidaita darajar Naira, da kuma karfafa tsaron makamashi.
Wannan ci gaba na rage farashi da kuma tabbacin wadatar mai, yana kawo sauki ga gidaje, ‘yan kasuwa, da masu sufuri a fadin kasa.
Matatar Dangote ta kuma fitar da gargadi mai karfi ga masu kokarin kirkirar karancin mai domin hana aiwatar da sabon farashin, tana kira ga hukumomin gwamnati su dauki mataki cikin gaggawa.
“Duk wani yunkuri na kirkirar karancin mai ko hana wadatar sa domin hana aiwatar da sabon farashi ba zai yuwu ba kuma ba za a yarda da shi ba. Muna bukatar hukumomin da ke kula da harkar su kasance cikin shiri su kuma dauki mataki cikin gaggawa, musamman a wannan lokaci na bukukuwa,” in ji sanarwar.
An shawarci masu amfani da mai da su guji sayen mai a farashi mai tsada idan akwai mai, mai inganci da araha a kusa.
“Muna karfafa gwiwar ‘yan Najeriya da su guji sayen PMS a farashi mai tsada idan suna iya samun mai da aka tace a cikin gida a ₦739 kowace lita daga fiye da tashoshin MRS 2,000 a fadin kasa. Ku kai rahoton duk wata tasha ta MRS da ke sayar da mai sama da ₦739 ta kiran lamabr wayan 0800 123 5264,” in ji matatar.
“Muna kuma kira ga sauran masu tashar mai da su sayi kayayyakinmu domin a yada amfanin wannan saukin farashi ga ‘yan Najeriya a dukkan tashoshi, domin samar da sauki mai fadi da kuma daidaita kasuwar man fetur.”
Matatar Man Fetur ta Dangote ta sake jaddada kudirinta na samar da mai cikin lokaci, daidaita farashi, da kuma tabbatar da tsaron makamashi, tana mai cewa ayyukanta na dogara ne da muradun kasa na dogon lokaci, ba matsin lamba na kasuwa na gajeren lokaci ba.
“Manufarmu ta kasance a bayyane, tabbatar da wadatar kayayyakin man fetur masu inganci a farashi mai sauki ga ‘yan Najeriya, tare da tallafa wa daidaiton tattalin arziki da rage dogaro da shigo da kaya daga waje,” in ji matatar a karshe.



















