Daga Bashir Bello, Abuja
Muhimmancin siyasar Farfesa Muhammad Sani Bello, wanda aka fi sani da Mainan Zazzau, ya sake zama abin muhawara mai zafi.
Biyo bayan yunkurin wasu magoya bayan APC na rage tasirinsa, mai taimaka masa na kafafen yada labarai, Joshua Danwana, ya bayyana wadannan kokarin a matsayin “tashin hankali da aka lullube da farfaganda,” yana kiran su aikin Sojojin Baka masu kare muradun APC.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa ’yan jarida a Kaduna, Danwana ya jaddada cewa Professor Bello wanda ya taba zama kwamishina sau uku kuma babban dan takarar gwamna a 2027 shi ne Wanda ya jagoranci nasarar Sanata Uba Sani a zaben gwamna na 2023. A cewarsa, nasarorin siyasar Bello suna ci gaba da tayar da hankali ga masu mulki da ke kara rasa kusanci da jama’a.
Sanarwar ta jaddada cewa Bello ya kasance Jagoran Nasarar 2023, amatsayin sa na Darakta Janar na Kwamitin Kamfen na Uba Sani a 2023. Zabensa bai zo da bazata ba; an dauke shi ne saboda karfin goyon bayan sa a matakin talakawa, dangantaka ta kasa da kasa, da kuma karfin jan hankalin masu kada kuri’a. Tare da cikakken goyon bayan tsohon Gwamna Nasir El-Rufai, Bello ya shimfida tubalin da ya kai ga fitowar Uba Sani a matsayin Gwamnan Kaduna duk da tsananin adawa.
“Wannan kamfen bai gudana da kansa ba. Bai ci nasara da bazata ba. Ya ci nasara ne saboda Mainan Zazzau ya tsara shi ya kuma kai shi daga tushe zuwa nasara,” in ji sanarwar. Da babu dabarun Professor Bello ba, APC da ta shiga zaben da rarrabuwar kawuna da rauni.
Yanzu yin ikirarin cewa Bello ba shi da tasiri, a cewar Danwana, “ko dai rashin gaskiya ne da gangan ko kuma sakaci na tunani.” Ya soki dogaro da ’yan cyber wajen yada karya, yana gargadin cewa irin wannan dabi’a na iya lalata makomar kyakkyawan mulki.
Sanarwar ta kara da cewa yunkurin nuna Bello a matsayin wanda ba shi da tasirin talakawa “abin tausayi ne kuma cin mutunci.”
Fiye da shekaru talatin, Bello ya zuba jari a fannin karfafa matasa, tallafin ilimi, jagoranci, da ci gaban al’umma a Sabon Gari da sauran wurare.
“Karfin talakawa ba a gina shi da kururuwar taken jam’iyya a taron ward ba,” in ji Danwana. “Ana gina shi ne da shekaru na kasancewa, shiga tsakani, da tallafi na zahiri. A wannan mizani, tarihin Bello ya fi kowace farfaganda magana.”
Ya jaddada cewa Abin da ya fi tayar da hankali ga APC shi ne ficewar Bello zuwa jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC). Murabus dinsa a matsayin kwamishina da mamba na majalisar zartarwa ta Kaduna a watan Yuli 2025 ya biyo bayan nada shi a matsayin mamba na kwamitin duba kundin tsarin mulki na ADC matakin da ya kara tabbatar da kimar siyasar sa.
Danwana ya jaddada cewa Bello ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa APC da kuma hawanta kan karagar mulki a Kaduna da Najeriya tun daga 2015. “Ba kawai mukaddashin kwamishina ba ne. Shi ne kwakwalwa da mai tsara injin siyasa mai cike da bukatu daban-daban,” in ji shi.
Yanzu da Professor Bello ya koma ADC, jam’iyyar mai mulki ta APC ta shiga halin “tashin hankali,” tana sane da cewa wannan mai dabarun da ya kai su ga nasara a 2023 na iya jagorantar faduwar su a 2027.
Ya ce Gaskiyar da Ba Za a Canza ba itace,
Ko da APC za ta yi kokarin sake rubuta tarihi, Danwana ya jaddada cewa babu wata farfaganda da za ta iya goge rawar Bello a nasarar Uba Sani ta 2023.
“’Yan siyasa Masu daukan nauyi Sojojin Baka su za su iya ci gaba da yaudarar kansu. Amma ba za su iya canza gaskiyar cewa nasarar Uba Sani a 2023 tana dauke da sahihin sa hannun Prof. Muhammad Sani Bello ba. Kuma babu wata farfaganda da za ta iya goge hakan,” in ji shi a karshe.





















