Daga Ahmed Hassan Ahmed, Abuja.
Reshen samar da man fetur na kamfanin NNPC Limited, ya kafa sabon tarihi da samar da ganga 355,000 na man fetur a rana, adadin da ya fi kowanne girma tun daga shekarar 1989.
Wannan nasara ta nuna ci gaba mai ma’ana a bangaren hakar mai na Najeriya, tare da tabbatar da sauye-sauyen da kamfanin ke yi bisa tushen inganci da tsari. Daga shekarar 2023 zuwa 2025, adadin samar da mai ya karu da kashi 52%, daga ganga 203,000 zuwa ganga 312,000 a rana.
Hakkan yana kunshe ne a wata Sanarwa dauke da sa hannun Andy Odeh, Ofishin Hulɗa da Jama’a, NNPC Ltd., Abuja
A cewar Sanarwan, Wannan ci gaba ba wai sakamakon sa’a ba ne, in ji kamfanin, amma yana da tushe a cikin dabarun aiki masu inganci, kula da kadarori yadda ya kamata, da kuma tsara filayen hakar mai cikin tsari. A cewar NEPL, wannan nasara ta nuna cewa da shugabanci nagari, tsarin aiki mai ƙarfi, da ma’aikata masu jajircewa, Najeriya na iya shawo kan matsalolin da suka dabaibaye bangaren mai na tsawon shekaru.
Shugaban kamfanin NNPC Limited, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana cewa wannan nasara alama ce ta cewa farfadowar bangaren makamashi a Najeriya Yana mai cewa ba mafarki ba ne amma gaskiya ce da ke faruwa yanzu.
“Ta hanyar nuna cewa tana iya wuce iyakar da ta sa wa kanta, NEPL ta tabbatar da cewa ginshikan da ake bukata don kara yawan samar da mai a kasa suna nan daram,” in ji Ojulari.
“Wannan nasara na nuna cewa injin samar da mai kayan aiki, hanyoyin aiki, ƙwarewa da haɗin gwiwa na iya aiki da tsari na kasuwanci don samar da sakamako mai kyau.”
Ojulari ya kara da cewa wannan ci gaba yana kara tabbatar da kwarin gwiwa a cikin gida da kuma a kasuwar makamashi ta duniya, yana tabbatar wa da abokan huldar Najeriya da masu zuba jari cewa kasar na da niyyar ci gaba da kasancewa amintaccen mai samar da makamashi.
Shima Udy Ntia, Mataimakin Shugaban Kamfanin mai kula da bangaren hakar mai (Upstream), ya ce wannan nasara ta wuce kawai adadin ganga 355,000.
“A bangaren da wasu ke amfani da hanyoyin gajeren lokaci don samun riba, NEPL na nuna wata hanya daban, ci gaba mai dorewa dole ne ya ta’allaka da aiki.
Wannan yana tabbatar da cewa kara yawan samarwa ba zai cutar da lafiyar ma’aikata, zaman lafiya a cikin al’umma, ko kare muhalli ba,” in ji Ntia.
Shima Daraktan NEPL, Nicolas Foucart, ya bayyana cewa wannan nasara ta NEPL tana wakiltar sauyi mai zurfi da ke gudana a fadin kamfanin NNPC Limited.
“Wannan labari ne da shugabanci mai hangen nesa ya tsara; da haɗin gwiwa bisa fahimta da amana; da kuma ma’aikata masu jajircewa da ke sauya buri zuwa nasarori da za a iya aunawa. Mutanenmu, hanyoyinmu da ƙa’idodinmu su ne ginshikan wannan nasara,” in ji Foucart.
Ya kara da cewa: “Ga ‘yan Najeriya, wannan nasara ba wai kawai karin yawan ganga ba ce; tana nufin karin kudaden shiga na kasa, karin tsaron makamashi, da kuma gindin tattalin arziki mai ɗorewa. NEPL ba wai kawai ta kara samar da mai ba; ta kuma farfado da kwarin gwiwa a cikin abin da bangaren makamashi na Najeriya zai iya cimma da tsarin da ya dace, al’ada mai kyau, da jajircewa.”
Kamfanin NNPC E&P Limited cikakken reshe ne na NNPC Limited da ke da alhakin bincike da hako albarkatun mai da iskar gas a Najeriya.



















