Daga Ahmed Hassan Ahmed
Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPC Limited, ta hannun Gidauniyar kamfanin, wato NNPC Foundation, ya samu babban yabo a gasar SERAS Africa Sustainability Awards karo na 19, inda aka karrama shi da lambar yabo ta “Kungiya Mafi Kishin Al’umma a Afrika.”
A yayin bikin da aka gudanar a Lagos, NNPC Foundation ta samu lambobin yabo guda biyar, ciki har da: Mafi Kyau a Fannin Samar da Ayyukan Yi da Ci gaban Tattalin Arziki, Mafi Kyau a Hulda da Masu Ruwa da Tsaki, Mafi Kyau a Yaki da Talauci, Gwarzon Ma’aikacin Ci gaban Dorewa na Afrika, Emmanuella Arukwe, da Babban Lambar Yabo ta Kungiya Mafi Kishin Al’umma.
A jawabin da ta gabatar a madadin hukumar NNPC, Babbar Darakta a sashen Business Services, Sophia Mbakwe, ta bayyana cewa wannan yabo hujja ce ta irin gudunmawar da NNPC ke bayarwa wajen ci gaban kasa.
Shugabar NNPC Foundation, Emmanuella Arukwe, ta bayyana cewa nasarorin da suka samu sun hada da:



















