Daga Bashir Bello,Abuja
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC Limited, ya tabbatar da cewa an samu nasarar shawo kan matsalar lalacewar wani sashe na bututun iskar gas na Escravos–Lagos (ELPS) da ke Kudu maso Yammacin Warri, Jihar Delta.
Lamarin, wanda aka samu rahotonsa a ranar Alhamis, 11 ga Disamba, 2025, yanzu an kawo shi ƙarƙashin kulawa, inda aka keɓe dukkan sassan bututun da abin ya shafa cikin tsaro domin kare lafiyar al’ummomin da ke yankin, ma’aikata, da muhalli.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi, NNPC Ltd ta bayyana cewa an gudanar da binciken farko a wurin da abin ya faru tare da haɗin gwiwar tawagogin fasaha daga kamfanin, Hukumar Kula da Harkokin Tsakani da Rarraba Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA), da kuma kamfanonin gyara.
Sanarwar ta ce, Kamfanin NNPC Gas Infrastructure Company (NGIC), wanda ke kula da gudanar da tsarin bututun, ya kunna Tsarin Ci gaba da Ayyuka (Business Continuity Plan) domin rage tasirin lamarin ga duk masu ruwa da tsaki, ciki har da masu jigilar iskar gas da masu samarwa.
NNPC Ltd ta jaddada cewa tana ci gaba da tattaunawa da al’ummomin da abin ya shafa, hukumomin jihohi, da sauran muhimman masu ruwa da tsaki, tare da nuna godiya ga goyon baya da haɗin kai da suke bayarwa.
Kamfanin ya kuma sake tabbatar da jajircewarsa wajen kare lafiyar al’ummomin da ke yankunan da yake aiki, kiyaye muhalli, da tabbatar da ingancin ayyukansa a dukkan kadarorinsa.
Sanarwar ta samu sa hannun Babban Jami’in Hulɗa da Sadarwa na NNPC Ltd, Andy Odeh, kuma an sanya mata kwanan wata 14 ga Disamba, 2025, a Abuja.



















