
Masu ruwa da tsaki da yan kasuwa a baje koli na Duniya na Kaduna karo na 47 sun samu karin haske kan tsare-tsaren dogon lokaci na Rukunin Dangote yayin da wakiliyar kamfanin, Fatima Wali Abdurrahman, ta bayyana taswirar burin kamfanin na Vision 2030.
A yayin jawabi a Ranar Musamman ta kamfanin, wadda ta jawo hankalin ’yan masana’antu, ’yan kasuwa da masu zuba jari, Hajiya Wali Abdurrahman ta bayyana shirin kamfanin na karfafa masana’antu a Najeriya da kuma inganta dogaro da kai ta hanyar samar da kayayyaki a cikin gida da kara darajar su.
Ta bayyana cewa Manufar 2030 ta kamfanin an tsara ta ne domin sanya rukunin ya zama babbar cibiyar masana’antu ta duniya tare da tallafawa ci gaban tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da ayyukan yi, amfani da fasaha da kuma fadada sarkar samar da kayayyaki.
Ta ce jarin kamfanin a muhimman fannoni kamar siminti, takin zamani, sinadarai, makamashi, sukari da gishiri na nufin rage dogaro da shigo da kaya daga waje da kuma karfafa masana’antu a cikin gida.
A cewarta, wannan dabarar ta yi daidai da kokarin gyaran tattalin arziki da aka tsara domin karfafa ci gaban masana’antu.
Hajiya Wali Abdurrahman ta jaddada cewa hangen nesa na dogon lokaci na kamfanin ya fi mayar da hankali kan hadin gwiwa da kananan da matsakaitan masana’antu, masu rarrabawa da masu samar da kayayyaki na cikin gida, inda ta yi nuni da cewa ci gaban masana’antu mai dorewa yana bukatar shiga daga kowane bangare na sarkar samar da kayayyaki.
“Tare da Rukunin Dangote, ci gaban abun cikin gida ba wani taken magana ba ne, shi ne ginshikin falsafar kasuwancinmu. Muna da yakinin cewa arzikin Najeriya dole ne ’yan Najeriya su gina shi, ta amfani da albarkatun Najeriya, domin amfanin al’ummomin Najeriya,” in ji ta.
Kamfanin ya kuma yi amfani da Ranar Musamman wajen kaddamar da sabbin nau’ikan marufin sukarin Dangote na 25kg da 100g a baje kolin.
A nasa jawabin, Shugaban Kaduna Chamber of Commerce Industry Mines and Agriculture (KADCCIMA), Farouk Suleiman, ya bayyana Rukunin Dangote a matsayin ba wai kawai wata kungiya ta kasuwanci ba, amma alamar kwarewar masana’antu.
Ya yaba da hadin gwiwar KADCCIMA da kamfanin, inda ya kara da cewa shiga da goyon bayan kamfanin a kai a kai na nuna imanin sa ga karfin baje kolin kasuwanci da sadarwa.
Sanarwar da Sashen Hulda da Jama’a na kamfanin ya fitar ta ce Dangote Cement, Dangote Sugar, NASCON Allied Industries (Dangote Salt), Dangote-Sinotruk, Dangote Peugeot Automobile, da Dangote Fertiliser sun halarci baje kolin, inda kowanne bangare ya kafa teburin taimako domin amsa tambayoyin abokan ciniki masu sha’awa.





















