
Daga Bashir Bello, Abuja
‘Yan kasuwa da mahalarta bikin kasuwanci na kasa da kasa da aka kammala a Kano sun yaba da sabbin buhunan sikari na Dangote da aka kaddamar, inda suka bayyana su a matsayin masu saukin amfani, masu dacewa da bukatun masu amfani, kuma sun dace da amfani a gida da kuma sayarwa.
Kamfanin Dangote Sugar ya kaddamar da sabbin girman buhuna, ciki har da na gram 100 da kuma buhun kilo 25, da nufin rage tsadar samunsu da kuma fadada kasuwa.
“Wadannan sabbin buhunan sikari na Dangote za su taimaka matuka wajen saukaka samun sikari ga talakawan jama’ar Arewa,” in ji Alhaji Isyaku Umar Tofa, Makaman Bichi, daya daga cikin sarakunan da suka halarci bikin, yayin da yake zantawa da manema labarai a Ranar Musamman ta kamfanin.
A cewarsa, sabbin buhunan da aka sake fasalta su da kuma farashi mai sauki za su bai wa gidaje da ‘yan kasuwa kanana da masu sayar da abinci damar samun sikari mai inganci ba tare da wahalar kudi ba, wanda hakan zai tallafa wa bukatun yau da kullum da kuma kananan harkokin kasuwanci.
A nasa bangaren, fitaccen dan kasuwa kuma Shugaban Kamfanin Sambajo General Enterprises Limited, Alhaji Salisu Sambajo, ya ce buhun kilo 25 ya dace da kananan masana’antu, masu yin burodi, gidajen cin abinci da masu rarraba kaya da ke bukatar sikari da yawa amma cikin farashi mai sauki.
Ya kara da cewa buhun gram 100 kuma an tsara shi ne domin gidaje masu karamin karfi, kananan shaguna da kuma masu bukatar sikari cikin gaggawa.
“Wadannan sabbin girman buhuna sun kara fadada damar mu wajen kaiwa ga kowane bangare na masu amfani, sun inganta ganin samfurin a kasuwannin bude da shaguna, kuma a karshe za su kara mana kaso a kasuwar Arewa,” in ji shi.
Dangote na daya daga cikin manyan masu daukar nauyin Bikin Kasuwanci na Kano, wanda taken sa shine: “Karfafawa SMEs Domin Ci Gaban Dorewa.”
Alhaji Sambajo ya jaddada cewa zuba jari da Dangote Group ke ci gaba da yi a muhimman bangarori kamar sikari, man fetur, siminti, takin zamani da sauransu ya taimaka matuka wajen ci gaban kasa da inganta rayuwar jama’a.
Ya bukaci Dangote da ya ci gaba da jajircewa wajen samar da inganci, kirkire-kirkire da karfafawa al’umma, musamman a yankunan Arewa.
“Gudummawar Alhaji Aliko ba ta da kamarsa, kuma muna fatan ganin karin nasarori da za su tallafa wa ci gaban Najeriya da dogaro da kai,” in ji shi.
Ya kuma bukaci gwamnati da ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga manyan masana’antu kamar Dangote Group.
“Muna bukatar manufofi masu tallafawa a fannin sufuri, haraji, wutar lantarki da saukin gudanar da kasuwanci domin wadannan masana’antu su ci gaba da aiki yadda ya kamata kuma su kasance masu gogayya a kasuwa,” in ji shi.
Wata ‘yar kasuwa daga Maiduguri, Hajiya Y’agana Babagana, wadda ta halarci bikin kasuwanci na Kano, ta bayyana shirin kamfanin na kaddamar da sabbin buhunan sikari masu saukin farashi na gram 100 da kilo 25 a matsayin ci gaba mai kyau ga masu amfani.
“Ina sayar da turaren wuta na gargajiya, kuma sikari muhimmin sinadari ne wajen hada shi. Ba za ka iya yin turaren wuta ba tare da sikari ba,” in ji Y’agana.
Ta bayyana farin cikinta da sabbin nau’ikan sikarin Dangote, tana mai cewa, “Ka ga dalilin da yasa muka yi tururuwa zuwa rumfar Dangote domin siye, musamman buhun kilo 25.”




















