


A wani muhimmin taron da ke nuna babban ci gaba a fannin binciken lafiya a Najeriya, Hukumar Kimiyyar Dakin Gwaje-gwaje ta Najeriya (MLSCN) ta karɓi sabunta Dakin Gwajin Inganci na Ƙasa (NEQAL) da ke Saye, a garin Zaria.
An gudanar da bikin mika dakin a ranar Litinin, 16 ga Disamba, 2025, inda manyan jami’ai daga gwamnati, abokan hulɗa na ci gaba, da ƙwararrun ma’aikatan dakin gwaje-gwaje suka halarta.
Yayin jawabin sa, Mukaddashin Rajistara kuma Shugaba na MLSCN, Dr. Donald Ibe Ofili, ya bayyana cewa wannan taron “ya fi kammala aikin gine-gine kawai.”
Ya jaddada cewa sabunta dakin NEQAL wata babbar mataki ce wajen ƙarfafa tabbatar da inganci, tsaron marasa lafiya, da kuma kwarewa a fannin binciken lafiya a duk faɗin Najeriya.
Dr. Ofili ya nuna godiya ga Gwamnatin Tarayya bisa ci gaba da zuba jari a fannin lafiya, yana mai cewa Manufar “ Shirin Sabon fata” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ta samar da ingantaccen tsarin gyaran harkar lafiya.
Ya yaba da jagorancin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a da kuma Ministan Ƙasar na Lafiya bisa yadda suka sauya wannan hangen nesa zuwa aiki.
Haka kuma, ya yaba da Hukumar Kula da Cutar Kanjamau ta Ƙasa (NACA) ƙarƙashin jagorancin Dr. Temitope Ilori, bisa yadda suka tafiyar da tallafin Global Fund RSSH2 da C19RM.
Mukaddashin rajistaran ya kuma nuna godiya ga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka (CDC) da Global Fund bisa goyon bayan su tun lokacin ƙaddamar da NEQAL a 2009, da kuma Cibiyar Nazarin Cutar Kanjamau ta Najeriya (IHVN) bisa taimakon fasaha da suke bayarwa.
A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, wanda Injiniya Jamil Ahmed Jaga, Shugaban Karamar Hukumar Zaria ya wakilta, ya yaba da NACA da Dr. Ilori bisa jagoranci nagari wajen sabunta dakin. Ya ce aikin ya yi daidai da Manufar Shirin Sabon fata ta gwamnatin Tinubu da kuma Manufofin Cigaban Dorewar (SDGs).
Kakakin ya sake jaddada kudirin Majalisar Tarayya na tallafawa gine ginen kiwon lafiya ta hanyar dokoki, kasafin kuɗi, da sa ido.
“Ƙasa mai lafiya ƙasa ce mai arziki,” in ji shi, yana mai alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, NACA, MLSCN, da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga kowa da kowa.
Dr. Tajudeen ya kuma yaba da rawar da Global Fund ke takawa wajen ƙarfafa ƙarfin binciken lafiya a Najeriya, musamman a yaƙi da cututtukan HIV, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro.
Haka zalika, Darakta Janar na NACA, Temitope Ilori, wanda Mallam Mustapha Yau, Mukaddashin Darakta na Kudi da Gudanarwa ya wakilta, ya gode wa dukkan abokan ci gaba da masu ruwa da tsaki bisa hangen nesan su wajen tallafawa sabunta da mika wannan daki, yana mai cewa dakin ya kai matakin ƙasa da ƙasa.
Kammala da mika sabunta dakin NEQAL na nuna sabon babi a ƙoƙarin Najeriya na cimma kwarewa a binciken lafiya ta hanyar ingantattun gine gine da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.














