Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja
Jigo a majalisar dattawa, Sanata Abdul Ningi daga Jihar Bauchi ya bayyana jin daɗinsa kan amincewa da Majalisar Dattawa ta yi wa Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro na Najeriya, yana mai cewa wannan nadin “kamar saka ƙwarya a ramin ta ne.”
Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan zaman tantace ministan, Sanata Ningi ya nuna kwarin gwiwarsa cewa Janar Musa zai iya fuskantar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta. Ya kwatanta shi da waɗanda suka riga shi a mukamin, yana cewa, “Shekaru biyu da suka gabata, tsofaffin gwamnoni da suka rike wannan mukami, ba za su iya bayar da abin da ba su da shi ba.”
“Janar Musa ya san matsalolin tsaro da hanyoyin magance su,” in ji shi. “Idan aka ba shi goyon baya, zai yi nasara.”
Sanatan ya kuma jaddada muhimmancin wannan nadin a fannin haɗin kai da zaman lafiya tsakanin addinai. “Wannan nadin ya nuna cewa Kiristoci a Najeriya ba a ware su ba bisa dalilin addini,” in ji shi. “Janar Musa mutum ne da kowa ke ƙauna, ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.”
Ya ƙara da cewa Janar Musa, wanda Kirista ne, ya rike mukamin Babban Hafsan Tsaro a wannan gwamnati, kuma an haife shi a Jihar Sakkwato. “Ya fahimci bambancin da ke Arewacin ƙasar nan, kuma baya nuna bambanci tsakanin addinai ko ƙabilu,” in ji Ningi.
Sanata Ningi ya yaba da Shugaba Bola Tinubu bisa nadin da ya yi wa Janar Musa, yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace kuma zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da haɗin kan ƙasa.
Dangane da dabarun tsaro, Ningi ya bayyana cewa sabon ministan ya amince da amfani da hanyoyin da ke haɗa amfani da ƙarfi da kuma tattaunawa Wanda zai hada da Shugabanin Alumma (kinetic da non-kinetic) wajen magance matsalolin tsaro. “Wannan yana nufin kowa ya sa hannu,” in ji shi.
Game da gyaran dokar hana ta’addanci da ta haɗa da satar mutane a matsayin laifi mai ɗauke da hukuncin kisa, Sanata Ningi ya ce hakan ya zama dole. “Lokacin da aka fara kafa wannan doka fiye da shekaru goma da suka wuce, masu garkuwa da mutane suna yin hakan ne don kuɗi. Amma yanzu suna kashe mutane ko da bayan sun karɓi fansa,” in ji shi. “Wannan gyara ya zama wajibi.”
Sanatan ya kuma bayyana cewa talauci na daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin tsaro, kodayake ya ce hakan ba hujja ba ce ta aikata laifi.
Sanata Ningi ya nuna fatan cewa ƙarƙashin jagorancin Janar Musa, Najeriya za ta samu zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.




















