Abubakar Ubale shi ne Shugaban Kamfanin MashaAllah Phone Accessories dake kusa da Babban Masallacin Bwari. A wannan tattaunawa ta musamman da dan jarida Ahmed Aliyu, ya bayyana irin fadi-tashin da ya fuskanta a harkar sayar da wayoyi, inda ya tona asirin kalubalen dake cikin sana’ar da kuma hadarin dake tattare da sayen wayoyin hannu (second-hand).
Ga dai yadda hirar ta kasance:
Tambaya: Ni daga News Global Enterprise da Kauwanci Duniya nake, muna tallata kananan sana’o’i a fadin kasa. Za ka iya ba mu takaitaccen tarihin ka?
Abubakar Ubale: Sunana Abubakar Ubale, ni dan jihar Kano ne. An haife ni a Sharada Phase 1 a Kano. Na yi makarantar boko a can, sannan na tafi makarantar Allo a jihar Jigawa inda na shafe shekaru 10. Na dawo Kano, sannan na nufi Abuja neman na kaina. Na fara zama a Tafa, sannan na koma Maje, daga karshe na dawo Bwari.
Na fara sana’ar ne da cajin waya, sannan na koma sayar da wayoyin hannu (second-hand). Amma Allah ya kawo ranar da na daina cajin waya da sayar da wadannan wayoyin saboda hadarin dake ciki. Na fuskanci kalubale da yawa a lokacin. Ina godiya ga Allah da ya fitar da ni daga wannan matakin zuwa matsayin mai sayar da sabbin wayoyi da kuma wadanda aka kera a kasashen waje (London-used).
Tambaya: Yaushe ka fara wannan sana’ar, kuma shekarunka nawa a ciki?
Abubakar Ubale: Na kusa shafe shekaru 20 ina wannan harkar ta waya.
Tambaya: Menene ra’ayinka game da sana’ar waya?
Abubakar Ubale: A gaskiya ina godiya ga Allah. Sana’a ce mai riba sosai, amma tana da hadari da kalubale. Babban abin da mutum yake bukata shi ne hakuri, rashin kwadayi, da kuma tsantsar taka-tsantsan. Kana iya tunanin cewa sayen wayar hannu mai arha daga wajen abokin ciniki riba ce, amma gaskiyar magana ita ce wannan cinikin zai iya jefa ka cikin bakin ciki da masifa.
Tambaya: Shin kana nufin sayen wayoyin hannu (second-hand) na da hadari?
Abubakar Ubale: Kwarai kuwa, yana da matukar hadari. Sayen wayar hannu na zuwa da babbar matsala, shi ya sa na daina ma’amala da su. Misali, kana iya sayen waya, idan maganar ta kai ga ‘yan sanda ko jami’an tsaro, sai abin ya zama wani abu daban. Kuna iya sayen waya a kan naira dubu goma, amma idan aka kai ka caji-ofis, sai a ce wayar da aka yi fashi da ita ce. Za ka iya tsinci kanka kana kashe kudin da suka ninka dubu goma kafin ka kubuta. Don haka, ina ribar take? Wani lokacin ma tarkon ne ake dana wa mutum. Wani bako zai zo ya sayar maka da waya yau, washegari wani ya zo ya ce tasa ce, kafin ka ankara ka tsinci kanka a hannun ‘yan sanda. Wannan ya sa na koma sayar da wayoyin “London-used” kawai.
Su wayoyi ne da ake shigo da su kai tsaye daga kasar waje. Muna da samfura kamar Oppo, Vivo, Huawei, Redmi, ZTE da sauran su. Dillalai ne halastattu suke shigo da su Najeriya. Mu kuma muna zuwa kasuwanninmu mu zaba, mu biya kudi, mu kawo shagonmu mu tsara su, sannan mu sayar wa kwastomominmu tare da ba su takardar shaida (receipt). Tambaya: Mai ribar sanar waya?
Abubakar Ubale: Ina godiya ga Allah da na shiga wannan sana’a. Na fara ta ne tun ina gwauro, amma ta dalilin ta na yi aure; na auri matata ta farko da ta biyu duka a cikinta. Yanzu ina da mata biyu da ‘ya’ya shida. Sannan na gina gidaje guda biyu duka ta dalilin wannan sana’a. Ina godiya sosai.
Tambaya: Wadanne kalubale kake fuskanta a matsayinka na wanda ya yi shekara 20?
Abubakar Ubale: Daya daga cikin manyan matsalolinmu shi ne rashin hadin kai a kungiyarmu ta masu sayar da wayoyi a nan Bwari. Akwai rikicin shugabanci da rashin fahimtar juna. Wannan ya sa ko gwamnati na son taimaka mana, ba za mu iya samu ba saboda rashin hadin kai. Wasu mambobin dake sayar da wayoyin hannu (second-hand) suna jawo mana matsaloli saboda rashin bin shawarwari da dokoki. Saboda haka, na gwammace na ware kaina in yi sana’ata da tsoron Allah.
Tambaya: Wayoyi nawa kake sayarwa a rana daya?
Abubakar Ubale: Ya danganta da yanayin kasuwa. Wata ranar ana iya sayar da waya goma ko fiye, wata ranar kuma ba za a sayar ko daya ba. Amma yanzu waya ta zama kamar abinci ga kowa, don haka ba kasafai ake zama ba tare da an sayar da ko daya ba.
Tambaya: Wane shawara kake da shi ga masu son shiga wannan sana’a?
A





















