
A taron bita na baje kolin kasa da kasa na Kaduna karo na 47 da aka gudanar a Rigachikun, Kaduna, a ranar 11 ga Fabrairu, 2026, manyan yan siyasa, shugabannin kasuwanci da masana sun tattauna kan makomar tattalin arzikin Najeriya a kan taken “Daga Sauye-sauye zuwa Sakamako: Sauyin Tattalin Arziki ta hanyar Ci gaban Abubuwan Cikin Gida da Dorewa.”
Rt. Hon. Aminu Bello Masari, tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Hukumar TETFund, ya jaddada cewa sauye-sauyen tattalin arziki da ci gaban abubuwan cikin gida su ne ginshikin dorewar tattalin arzikin Najeriya.
Ya bayyana cewa TETFund zai saka Naira biliyan 10 a shirye-shiryen bunkasa kwarewa a shekarar 2026 domin tallafawa kamfanonin cikin gida da kirkire-kirkiren ‘yan kasa.
A nasa jawabin, Alhaji Farouk Suleiman Farsman, Shugaban KADCCIMA, ya gode wa mahalarta da manyan baki, tare da yabawa Masari bisa jagorantar taron. Ya kuma jaddada cewa ci gaban abubuwan cikin gida ba zaɓi ba ne, illa wajibi ne domin dorewar tattalin arzikin Najeriya da gogayya a matakin duniya.
Ya kara da cewa taron baje kolin ba wai nune-nune da kasuwanci kadai ba ne, amma dandalin tattaunawa da samar da mafita ga matsalolin tattalin arziki. A cewarsa, “A nan ne manufofi ke haduwa da aikace-aikace, kuma ra’ayoyi ke zama mafita masu amfani.”
Farsman ya bukaci mahalarta da su bayar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen tsara manufofi da dabaru domin hanzarta ci gaban tattalin arzikin Kaduna da Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma yaba wa KADCCIMA bisa jajircewarta wajen ci gaba da gudanar da baje kolin duk da kalubalen tattalin arziki, yana mai cewa wannan juriya ta cancanci yabo.





















