Daga Bashir Bello
Yayin da aka Fara Buga gangar siyasa a sassan kasar nan, wani muhimmin ci gaban siyasa na kara bayyana a Jihar Zamfara, inda tsoffin masu rike da mukaman siyasa daga jam’iyyu daban daban suka fara hada kai da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bayan wani babban taron tattaunawa da Alhaji Atiku Abubakar Saleh, Baraden Maru kuma Mataimakin Sakataren Tsare tsare na Kasa na jam’iyyar ADC, ya jagoranta.
Taron ya hada tsoffin yan majalisar dokoki na jiha, tsoffin kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, shugabannin kananan hukumomi da kansiloli. Wannan taro ya zama dandalin tattaunawa, nazari da tsara dabarun siyasa. Wadannan gogaggun yan siyasa daga jam’iyyu daban daban sun tattauna yadda za su hada kai da jam’iyyar ADC domin cimma burin samar da jagoranci mai ma’ana a Jihar Zamfara.
Atiku Abubakar Saleh, wanda sunansa ya zama tamkar alamar hada kan jama’a daga tushe, ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana manufofin jam’iyyar da kudurinta na samar da shugabanci na kowa da kowa. Ya jaddada cewa ADC ba kawai jam’iyyar siyasa ba ce, illa kuwa wata tafiya ce da ke da ginshiki a kan gaskiya, rikon amana da sabunta tsarin kasa.
“ADC jam’iyya ce da ke tsaya tsayin daka wajen tabbatar da shugabanci na gari, kaunar mata da matasa, da kuma mayar da hankali kan farfado da tattalin arziki, musamman a wannan lokaci mai sarkakiya a tarihin kasarmu inda rashin tsaro ya zama ruwan dare,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga tsoffin masu rike da mukamai da su kawo kwarewarsu da dangantakarsu domin karfafa gindin jam’iyyar da fadada tasirinta. Haka zalika, ya bukaci matasa da mata na Jihar Zamfara da su mara wa ADC baya, yana mai jaddada cewa goyon bayansu na da matukar muhimmanci wajen gina zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
“Ba za mu iya gina sabuwar Zamfara mai inganci ba, Idan ba tare da kuzarin matasa da hikimar mata ba. Goyon bayan ku shi ne ginshikin da za mu gina sabon zamani na zaman lafiya, ci gaba da wadata,” in ji shi da kwazo.
Wannan taron tattaunawa na daga cikin jerin tarurrukan tuntuba da kungiyar Baraden Maru Youths Coalition Consultations Team (BMYCCT) ke jagoranta, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen karfafa goyon bayan jam’iyyar ADC a kananan hukumomi goma sha hudu (14) na Jihar Zamfara.
Wadannan tarurruka sun riga sun haifar da gagarumin sakamako, inda, da dama daga cikin masu ruwa da tsaki suka bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar karkashin jagorancin Atiku Abubakar Saleh.
Hon. Anas Ibrahim Diila, Shugaban BMYCCT na Jihar Zamfara, ya bayyana godiyarsa da cewa:
“Muna mika godiya ta musamman ga Alhaji Atiku Abubakar Saleh bisa jajircewarsa, hangen nesansa da sadaukarwarsa wajen bunkasa jam’iyyar. Taron da ya gudanar da jama’armu ya kasance abin alfahari da shaida ce ta yadda yake da kishin hadin kai da shugabanci na kowa da kowa.”
Nasara da aka samu a wannan taro ta samu ne da taimakon Hon. Shehu Maishanu, Jagoran Hadin Gwiwar ADC a Jihar Zamfara, wanda aka yaba masa bisa juriya da kwarewarsa wajen tsara tarurrukan. Haka kuma, Hon. Kabiru Garba Gusau, Shugaban jam’iyyar ADC na jihar, ya samu yabo bisa jagoranci mai nutsuwa da jajircewarsa wajen tabbatar da hadin kai a cikin jam’iyyar.
Yayin da jam’iyyar ADC ke kara samun karbuwa a Jihar Zamfara, jagorancin Atiku Abubakar Saleh ya zama haske mai nuna mafita, alamar sabon salo na siyasa da ke jan hankalin masu neman canji da ci gaba mai ma’ana.



















