Marubuci,Nicola Shubrook
Mene ne ƴaƴan cashew?
Ƴaƴan cashew wasu na’ukan abinci ne dangin gyaɗa da ake samu daga cikin cikin cashew.
Suna cikin rukunin ƴaƴan itatuwa da ake kira a nazarin kimiyyar tsirrai da Anacardiaceae, kamar su mangoro da sauransu.
Ƙasashen India da Vietnam na cikin ƙasashen da suka fi noma cashew a duniya, kuma ya fi samun tagomashi a wuraren da ke da danshi.
Sinadaran gina jiki da ke cikin ƴaƴan cashew166 kcal/695 kJ sinadarin ƙara kuzari
5.5g na sinadarin protein
13g na maiƙo
9g na sinadarin carbohydrates
1g na sinadarin fibre.
2 mg na iron
88 mg na magnesium
1.7 mg na zinc
La’akari da sinadaran abinci da ke cikin cashew, za a iya cewa abinci ne mai ɗauke da ɗimbin sinadaran protein da maiƙo mai inganci ga jiki.
A duk giram 30 na ƴaƴan cashew, akwai kusan sinadarin ƙara kuzari jiki da ya kai 160 a ma’aunin calories, sai kuma protein da sauran sinadaran da suke inganta lafiya.
Amfanin ƴaƴan cashew ga lafiya Rage maiƙo mai illa da ƙanƙancewar jijiya mai isar da jini sassan jiki
Ƴaƴan cashews na ɗauke da sinadarin folate da vitamin E, waɗanda suke taimaka wajen rage cushewar jijiyoyi masu isar da jini zuwa sassan jiki. Wani bincike da aka yi a shekarar 2019 ya nuna cewa cin ƴaƴan cashew a kullum na rage yawan maiƙo a jikin masu fama da cutar dieabetes nau’i na biyu.Inganta rayuwa
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa cimakan da ke ɗauke da maiƙo masu kyau irin su cashew suna taimakawa wajen rage cututtuka da dama suke barazana ga rayuwa.
3. Rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya da borin jini
Sinadaran homocysteine nau’i ne na amino acid, wanda idan ya yi yawa a jiki, yana janyo kumburi da ke kai wa ga ciwon zuciya ko borin jini. An gano cin ƴaƴan cashew na rage sinadarin na homocysteine a jiki.
6. Rage kumburin hanji
Bincike ya gano cewa cin ƴaƴan cashew na da alaƙa da rage kumburin hanji.
7. Rage ƙiba cikin sauƙi
Bincike ya gano cewa cimaka mai ɗauke da ƴaƴan cashew na taimakawa wajen rage ƙiba.
8. Kula da yanayin suga a cikin jini
Wani bincike da aka yi a 2019 ya nuna cewa cin ƴaƴan cashew a kullum yana inganta aikin sinadarin insulin, wanda shi ne yake taimakawa wajen rage sukarin da ke cikin jini wato cutar diabetes.
9. Rage ɗimuwa A cikin ƴaƴan cashew akwai sinadarai irin su vitamin da minerals da suke haɗuwa suna aiki tare domin rage ɗimuwa.
Kowa zai iya cin ƴaƴan cashew?
Ba mamaki jikin wasu ya kasance ba ya son ƴaƴan cashew, ko kuma idan sun ci, cikin su ya juya ko kuma jikin baki ɗaya ya samu canji, kamar kumburin fuska da kumburi a harshe da laɓɓa, idan aka samu matsala irin wannan, to a garzaya asibiti.
Sannan waɗanda ba sa son gyaɗa akwai yiwuwar ba za su so ƴaƴan cashew ba.
Amfani na musamman
Ƴaƴan cashew na da amfani sosai ga lafiya saboda suna ɗauke da sinadarai masu muhimmanci wajen gina jiki.
Sai dai duk da irin amfani da ake samu, akwai buƙatar a riƙa ci bisa ƙa’ida da samar da daidaito.
An fi so a ci tsabarsu ba tare an haɗa da gishiri ku zuma ba, ko kuma a ce sai an soya da zuma, domin guje wa rasa abin da ake buƙata. Credit :BBCC Hausa













