Daga Bashir Bello
Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bar Najeriya zuwa Saudiyya a wata ziyarar aiki.
Ahmad Muazu, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai a Ofishin Shugaban ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Muazu ya bayyana cewa, “Ziyarar na da nufin kammala shirye-shiryen karshe na Hajjin shekarar 2026 bisa tsarin aiki da aka amince da shi.”
Ya kara da cewa ma’aikatan ofishin NAHCON na shiyyar Kano, karkashin jagorancin Ko’odinetan shiyyar, Malam Umar Kalgo, ne suka raka shugaban yayin tafiyarsa.
















