• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Labarai

Kamfanin Siminti ta Dangote Cement Ta Kaddamar da Sansanonin Tsaro a garuruwan Jihar Kogi

Daga Bashir Bello

February 19, 2026
in Labarai
Reading Time: 2 mins read
0
Kamfanin Siminti ta Dangote Cement Ta Kaddamar da Sansanonin Tsaro a garuruwan Jihar Kogi
0
SHARES
15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Daraktan Masana’antar Dangote Cement Obajana, Injiniya Azad Nawabuddin, yana bayyana sansanin tsaro da kamfanin ya bayar ga al’ummar Apata Ipatun a Jihar Kogi, yayin da Mai Martaba Oba Frederick Balogun da Babban Manajan Sashen Zamantakewa na Al’umma, Prince Adeyemi Ademola, ke kallon abin da ya faru a karshen mako.
A wani bangare na jajircewarta wajen inganta tsaro da karfafa aikin ‘yan sanda na al’umma a cikin garuruwan da Kamfanin take gudanar da ayyuka.

Kamfanin Dangote Cement Plc, ta hannun katafaren offishin Obajana, ta kaddamar da sansanonin tsaro guda biyu a al’ummomin Iwaa da Apata.

Karanta HakananPosts

KAMFANIN DANGOTE CEMENT YA KADDAMAR DA KATAFAREN ASIBITI A JIHAR KOGI

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Garo a Matsayin Abokin Takararsa Domin Neman Zaben 2027

Gwamna Yusuf Ya Taya Shugaba Tinubu Murna Kan Mika Fom ɗin Neman Takarar INEC

Yayin da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Daraktan Masana’antar Obajana na Dangote Cement Plc, Azad Nawabuddin, ya bayyana cewa an aiwatar da ayyukan ne a matsayin wani bangare na jajircewar kamfanin wajen ci gaban al’umma da karfafa tsaro a cikin al’ummomin da ke karɓar bakin Kamfanin, ya ce ko da yake Iwaa tana da nisa da Kamfanin, al’ummar na da matsayi na musamman a cikin abubuwan da kamfanin ke bai wa muhimmanci, yana mai cewa kamfanin yana da cikakken shiri wajen tabbatar da cewa ayyukan ci gaba da tsaro sun wuce al’ummomin da ke kusa da ita.

Azad Nawabuddin ya jaddada cewa tsaro na da matukar muhimmanci wajen ci gaba da dorewar cigaban al’umma, yana mai cewa “al’umma da ba ta da tsaro ba za ta iya samun ci gaba mai ma’ana ba.”

Ya kara da cewa sabbin gine-ginen tsaro da aka kaddamar sun zama wani muhimmin mataki wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da karfafa dangantaka tsakanin al’ummomin da Dangote Cement Plc wajen gudanar da tsarin tsaro.

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Olu na Apata, Oba Fredrick Balogun, ya nuna godiya ga kamfanin bisa samar da abin da ya kira gine-gine masu kayatarwa da sauran abubuwan more rayuwa ga al’ummar Apata, yana mai cewa an saka al’ummar cikin jerin wadanda ke amfana da tallafin tsaro daga Dangote.

Hakazalika, Ya bayyana Alhaji Aliko Dangote a matsayin Wanda keda zuciya mai kyau kuma wanda Allah ya aiko wa mutanensa.

A nasa jawabin, Elesho na Iwaa, Mai Martaba Obafemi Abel Alade Alaofin, ya nuna godiya bisa abin da ya kira “nuna soyayya” daga Dangote Cement Plc.

Sarkin ya ce, al’ummarsa na matukar godiya da sabuwar cibiyar tsaro, yana mai alkawarin cikakken goyon baya ga kamfanin.

Ya ce Iwaa ta samu dimbin fa’ida daga Dangote Cement Obajana, yana mai cewa dangantakar da ke tsakanin su tana da kyau kuma suna amfanar juna.

Babban Manaja na Sashen Ayyukan Zamantakewa, Prince Adeyemi Ademola, ya ce binciken bukatu da aka gudanar a shekarar 2024 ya nuna cewa gine-ginen tsaro na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a al’ummomin Apata da Iwaa.

Prince Ademola ya ce a matsayin kamfani mai daukar nauyin zamantakewa, Dangote Cement Plc ta fara da kuma kammala ayyukan sansanonin tsaro don cika wannan bukata ta al’umma.

Ya sake jaddada jajircewar kamfanin wajen ci gaban al’umma mai dorewa ta hanyar ci gaba da tattaunawa da kuma aiwatar da ayyuka bisa fifiko.

Comrade Rotimi Kekereowo, Shugaban Matasa daga al’ummar Iwaa, ya nuna godiya ga kamfanin tare da kira da a ci gaba da hadin gwiwa don ci gaban al’umma.

A nasa bangaren, Sakataren al’ummar Apata, Comrade Adekunle Babatunde, ya gode wa Daraktan Shukar bisa daukar lokaci daga cikin jadawalin aikinsa don kaddamar da kuma mika sansanin tsaro, yana mai alkawarin cewa al’ummar za ta yi amfani da shi yadda ya kamata.

Previous Post

Rukunin Dangote Ya Haskaka Manufar 2030 a Taron Kasuwanci na Kaduna

Next Post

SAKON RAMADAN DAGA KASUWANCINDUNIYA.COM

Related Posts

KAMFANIN DANGOTE CEMENT YA KADDAMAR DA KATAFAREN ASIBITI A JIHAR KOGI
Labarai

KAMFANIN DANGOTE CEMENT YA KADDAMAR DA KATAFAREN ASIBITI A JIHAR KOGI

July 13, 2026
Gwamna Yusuf Ya Kai Ziyaran Gaisuwa da Girmamawa ga Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Ya Taya Shi Murna Bisa Fitowarsa a Matsayin Abokin Takaran Tinubu
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Garo a Matsayin Abokin Takararsa Domin Neman Zaben 2027

July 13, 2026
Gwamna Yusuf Ya Taya Shugaba Tinubu Murna Kan Mika Fom ɗin Neman Takarar INEC
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Taya Shugaba Tinubu Murna Kan Mika Fom ɗin Neman Takarar INEC

July 11, 2026
Gwamna Yusuf Ya Yi Kira Ga Matasa Lauyoyi Su Rungumi Gaskiya da Adalci
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Yi Kira Ga Matasa Lauyoyi Su Rungumi Gaskiya da Adalci

July 10, 2026
Gwamna Yusuf Ya Lashe Lambar Yabo Ta Ƙungiyar Matasa Lauyoyin Arewa
Labarai

Gwamna Yusuf Ya Lashe Lambar Yabo Ta Ƙungiyar Matasa Lauyoyin Arewa

July 10, 2026
RUNDUNAR YAN SANDAR JIHAR KADUNA SUN YI ALLAH WADAI DA KISAN GILLA DA AKAYI MA WASU MATAFIYA, SUN KAMA MUTUM 6 KAN KASHE MUTUM 2 MARASA LAIFI
Labarai

RUNDUNAR YAN SANDAR JIHAR KADUNA SUN YI ALLAH WADAI DA KISAN GILLA DA AKAYI MA WASU MATAFIYA, SUN KAMA MUTUM 6 KAN KASHE MUTUM 2 MARASA LAIFI

July 9, 2026
Next Post
SAKON RAMADAN DAGA KASUWANCINDUNIYA.COM

SAKON RAMADAN DAGA KASUWANCINDUNIYA.COM

SULE LAMIDO – JAGORA NA GASKIYA DA AKE JIRA

SULE LAMIDO – JAGORA NA GASKIYA DA AKE JIRA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
KAMFANIN DANGOTE CEMENT YA KADDAMAR DA KATAFAREN ASIBITI A JIHAR KOGI

KAMFANIN DANGOTE CEMENT YA KADDAMAR DA KATAFAREN ASIBITI A JIHAR KOGI

July 13, 2026
Gwamna Yusuf Ya Kai Ziyaran Gaisuwa da Girmamawa ga Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Ya Taya Shi Murna Bisa Fitowarsa a Matsayin Abokin Takaran Tinubu

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Garo a Matsayin Abokin Takararsa Domin Neman Zaben 2027

July 13, 2026
Gwamna Yusuf Ya Kai Ziyaran Gaisuwa da Girmamawa ga Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Ya Taya Shi Murna Bisa Fitowarsa a Matsayin Abokin Takaran Tinubu

Gwamna Yusuf Ya Kai Ziyaran Gaisuwa da Girmamawa ga Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Ya Taya Shi Murna Bisa Fitowarsa a Matsayin Abokin Takaran Tinubu

July 13, 2026
Gwamna Yusuf Ya Taya Shugaba Tinubu Murna Kan Mika Fom ɗin Neman Takarar INEC

Gwamna Yusuf Ya Taya Shugaba Tinubu Murna Kan Mika Fom ɗin Neman Takarar INEC

July 11, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by
►
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
►
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
►
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
►
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
►
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by