Daga Bashir Bello, Abuja
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta yi Allah wadai da lamarin kashe mutane biyu marasa laifi a hannun jama’a a kauyen Gidan Kalu dake yankin Birnin Yero, tare da tabbatar da kama mutum 6 da ake zargi da hannu a cikin kisan.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar a ranar 6 ga Yuli, 2026, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Yuli, 2026.
A cewar sanarwar, wadanda abin ya shafa sun hada da Muhammadu Sani mai shekara 45, da abokinsa Aliyu Mohammed mai shekara 40, duka ‘yan kauyen Umar na karamar hukumar Igabi. Suna kan hanya ne da babur zuwa Tudun Wada Zaria domin ziyartar kawun su da ke rashin lafiya.
Yayin da suke wucewa ta kauyen Gidan Kalu, wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun yi zargin su bayan ganin sabon babur da suke hawa, sai suka fara kuka da cewa “yan fashi ne”. Saboda tsoro, wadanda abin ya shafa suka bar babur din suka gudu. Sai dai taron jama’a masu fushi suka bi su, suka yi musu duka mai tsanani har suka kashe su, duk da bayanin da suka yi na cewa ba ‘yan fashi ba ne kuma wasu daga cikin masu kai musu hari ma sun san su.
Da samun rahoton, ‘yan sandan dake ofishin Birnin Yero suka gaggauta zuwa inda suka kama wadannan mutum 6 da ake zargi da hannu a cikin kisan:
1. Abdullahi Mukailu Kigo da wasu 5.
‘Yan sandan sun ce wadanda ake zargin sun furta aikata laifin kuma suna hannu yanzu, yayin da bincike ke cigaba da gudana domin gano da kama sauran wadanda suka halarci wannan kisan ba bisa ka’ida ba.
A nasa bangaren, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, psc, mni, ya yi Allah wadai da wannan mummunar dabi’a. Ya ce duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin, ba tare da la’akari da matsayinsa ba, za a kama shi a gurfanar da shi a gaban shari’a.
CP din ya gargadi jama’a da su daina daukar doka a hannu wato “jungle justice” bisa zargi kawai.
“Babu wani mutum da ke da hurumin zama mai bincike. A bisa doka, ana daukar wanda ake tuhuma da cewa ba shi da laifi sai an tabbatar da akasin hakan,” in ji shi.
Ya bukaci al’ummar jihar da su rika kai rahoton duk wani wanda ake zargi da aikata laifi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wasu hukumomin tsaro domin a yi bincike da gurfanar da su.




















