
Daga Bashir Bello, Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga matasa lauyoyi da su tsaya kan gaskiya, jarumta da kuma sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukan sana’arsu.
Wannan sanarwa ta fito ne daga mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Alhamis.
Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da yake bude taron shekara na biyu na Ƙungiyar Matasa Lauyoyin Arewa da aka gudanar a Amani Event Centre, Kano.Ya bayyana taken taron, “Taking a Stand” a matsayin mai dacewa da lokaci, yana mai jaddada muhimmancin jarumta, nauyin alhaki da jagoranci na ɗabi’a wajen fuskantar ƙalubalen da ke addabar sana’ar lauya.
Gwamna Yusuf ya shawarci matasa lauyoyi da su zabi gaskiya maimakon cin mutunci, jarumta maimakon tsoro, da hidima maimakon son kai.
Haka kuma ya yi kira ga manyan membobin Bar da Bench da su ƙarfafa tsarin ba da shawara da jagoranci ga matasa, tare da umartar lauyoyi da su tsaya kan bin doka da kare mutuncin tsarin shari’a yayin da ake shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Gwamnan ya gode wa Ƙungiyar bisa zaɓar Kano a matsayin wurin taron, da kuma ba shi lambar yabo ta kwarewa a jagoranci da hidima ga jama’a.
Ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa bangaren shari’a da kuma inganta bin doka.
A jawabinsa, Shugaban Ƙungiyar, Umar A. Chiroma, ya yaba wa Gwamnatin Kano bisa goyon bayan da ta bayar wajen nasarar gudanar da taron.
Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar Kano, Barrista Abdulkarim K. Maude, ya kuma yaba da gyare-gyaren da Gwamna Yusuf ya kawo a bangaren shari’a, ciki har da naɗin mace ta farko a matsayin Babban Alkalin Jihar, naɗin alkalai tara, da kuma ɗaukar ma’aikatan shari’a 70 a cikin Ma’aikatar Jihar Kano.
Taron ya samu halartar wakilin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima; wakilin Gwamnan Jihar Yobe; membobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano; jami’an kotu; lauyoyi; da matasa lauyoyi daga sassan Arewacin Najeriya.




















