• Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy
Kasuwancin Duniya
Advertisement
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
No Result
View All Result
Kasuwancin Duniya
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
  • Al’adu da Fasaha
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni
Home Kasuwanci

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ƙara Ƙaimi Wajen Kare Lafiyar Direbobi A Faɗin Afirka

October 25, 2026
in Kasuwanci
Reading Time: 4 mins read
0
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ƙara Ƙaimi Wajen Kare Lafiyar Direbobi A Faɗin Afirka
0
SHARES
7
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsApp

Shugaban Harkokin Sufuri na Kamfanin Siminti na Dangote, Murilo Silva (a hagu), da Babban Manajan Daraktan Kamfanin na Rukuni, Arvind Pathak (a dama), suna miƙa lambar yabo ga ɗaya daga cikin direbobin kamfanin yayin taron wayar da kan direbobi kan kare kai, wanda aka gudanar a masana’antar kamfanin da ke Obajana.

Karanta HakananPosts

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

Ba Wani Kudin Daya Bace Ko Ba A Biya Ba Ko Ba A Lissafa Shi Ba – NNPC Ta Yi Karin Bayani

Daga BAshir Bello, Abuja

Kamfanin Siminti na Dangote, wanda ke cikin manyan kamfanonin samar da siminti a Afirka, ya ƙara ƙaimi wajen inganta tsaron ababen hawa ta hanyar ɗaukar matakan ƙara wayar da kan direbobi, haɓaka ƙwarewarsu da tabbatar da bin ƙa’idojin tuƙi cikin aminci a dukkan rassansa da ke faɗin nahiyar.

Da yake jawabi a taron Horaswa da Wayar da Kan Direbobi Kan Kare Kai na Shekarar 2026, wanda aka gudanar a masana’antar kamfanin da ke Obajana, Jihar Kogi, Babban Manajan Daraktan Kamfanin na Rukunin Afirka, Mista Arvind Pathak, ya jaddada muhimmancin direbobi su riƙa yin tunani kan kare kai tare da tabbatar da tuƙi cikin aminci a duk inda kamfanin ke gudanar da ayyukansa a Afirka.

Pathak ya sake tabbatar da ƙudurin kamfanin na kare lafiyar direbobinsa da inganta jin daɗinsu. Ya kuma buƙace su da su ba da fifiko ga tuƙi cikin aminci, tare da tabbatar da cewa sun koma gidajensu lafiya bayan kowace tafiya.

A cewarsa, kasancewar Kamfanin Simintin Dangote shi ne kamfanin da ya fi samar da siminti a Nijeriya da Afirka, yana ba da muhimmanci sosai ga ingancin kayayyakinsa. Ya ce direbobin kamfanin na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da isar da simintin ga abokan ciniki cikin aminci da inganci.

Pathak ya jaddada cewa babu wata hajjar kasuwanci ko gaggawar kai kaya da ta kai darajar rayuwar ɗan Adam, yana mai cewa kare lafiyar direbobi ya fi muhimmanci fiye da cimma burin aiki ko la’akari da ribar kasuwanci.

Taron, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken “Ka Yi Tunani Kan Kare Kai, Ka Yi Tuƙi Cikin Aminci”, ya haɗa direbobi, ma’aikatan sufuri da wakilan shugabannin kamfanin domin ƙarfafa tuƙin da ya dace, tattauna matsalolin jin daɗin ma’aikata da kuma inganta al’adar ɗaukar matakan kare kai a harkokin jigilar kayayyakin kamfanin.

Da yake magana da mahalarta taron, Pathak ya tunatar da direbobin cewa su ne ke wakiltar sunan kamfanin Dangote a manyan titunan ƙasar, saboda haka suna da alhakin kare rayukansu da na sauran masu amfani da hanyoyi.

Ya ce, “Duk lokacin da ku ka hau mota domin tuƙi, ba kaya kawai ku ke ɗauka ba. Kuna ɗauke da martabar kamfanin nan, amincewar sauran masu amfani da hanya, kuma mafi muhimmanci, rayukanku. Za mu iya maye gurbin babbar mota, amma ba za mu iya maye gurbin ɗan Adam ba.”

Ya tabbatar wa direbobin cewa kamfanin zai ci gaba da zuba jari a shirye-shiryen inganta jin daɗinsu, haɓaka ƙwarewarsu ta sana’a da kuma tabbatar da cewa ayyukan sufuri suna gudana cikin aminci.

A cewarsa, direbobi na da muhimmiyar rawa a ci gaban kamfanin da tsarin rarraba kayayyaki, don haka kare lafiyarsu da walwalarsu na daga cikin abubuwan da kamfanin ya ba wa fifiko.

Pathak ya ce: “Muna godiya da sadaukarwar da kuke yi a kullum domin tabbatar da ci gaban kasuwancinmu. Shi ya sa muka himmatu ba kawai wajen samar muku da kayan aiki da horon da za su taimaka muku yin aiki cikin aminci ba, har ma da sauraron damuwoyinku da inganta jin daɗinku. Idan direbobinmu suna cikin aminci, ayyukanmu za su ƙara ƙarfi, al’ummomin da muke aiki a cikinsu kuma za su fi samun tsaro.”

Ya buƙaci direbobin su guji gudun wuce gona da iri, tuƙi cikin gajiya da sauran halayen tuƙi masu haɗari. Ya jaddada cewa ya kamata a auna ƙwarewar direba ta yadda ya isa inda zai je cikin aminci, ba da saurin da ya yi tafiyar ba.

Shugaban kamfanin ya kuma shawarci direbobi da su riƙa tsayawa su huta duk lokacin da suka ji gajiya, tare da guje wa shiga haɗarin da ba dole ba a kan hanya.

Ya ƙara da cewa, “Ina son kowane direba ya riƙa tunawa da wata muhimmiyar ƙa’ida guda ɗaya: idan ka gaji, ka tsaya ka huta. Idan ka ga wani yanayi ba shi da aminci, kada ka yi ganganci. Manufar tafiya ba kawai isa inda za ka je ba ce; manufar ita ce ka koma gida lafiya, ka haɗu da iyalinka.”

Shi ma shugaban harkokin sufuri na kamfanin Siminti na Dangote, Murilo Silva, ya gargaɗi direbobi kan tuƙi na ganganci, tuƙin da wani ke yi a madadin direban da aka ba aikin, da sauran hanyoyin gudanar da sufuri marasa aminci. Ya bayyana cewa kamfanin ba zai lamunci irin waɗannan ayyuka ba.

Silva ya buƙaci direbobin su ɗauki alhakin ayyukansu da kansu, tare da bayar da gudummawa wajen inganta tsaron hanyoyin Nijeriya ga masu ababen hawa da sauran masu amfani da tituna.

A nata jawabin, Ebere Okonkwo, shugabar harkokin sufuri, lafiya, tsaro da muhalli ta rukunin kamfanin na Afirka a Nijeriya, ta bayyana cewa gudanar da taron yana da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiyar direbobi da kuma hana aukuwar haɗurra da ka iya jawo korarsu daga aiki.

Ta ce taron zai taimaka wajen sa direbobin su ƙara taka-tsantsan, domin shugabannin kamfanin na sa ido kan zirga-zirgarsu a duk inda suka je.

Taron ya kuma ba direbobi damar tattaunawa kai tsaye da shugabannin kamfanin kan matsalolin da suka shafi jin daɗinsu da yanayin aikinsu.

Daga cikin abubuwan da suka gabatar akwai hauhawar tsadar rayuwa, kuɗaɗen da suke kashewa wajen gudanar da ayyukansu da kuma buƙatar a riƙa sanar da su sakamakon gwajin ƙwayoyi cikin lokaci.

Wasu daga cikin direbobin da suka halarci taron sun yaba wa kamfanin bisa ci gaba da zuba jari wajen inganta jin daɗinsu. Sun ce taron ya nuna cewa shugabannin kamfanin na damuwa da rayuwarsu, ba wai kawai aikin da suke gudanarwa ba.

Sun kuma yi alƙawarin ci gaba da bin ƙa’idojin tsaro, da kula da manyan motocin da aka damƙa musu kamar muhimman kadarorin kasuwanci, tare da guje wa duk wani hali da zai iya jefa rayukan jama’a cikin haɗari.

A ƙarshen taron, kamfanin Siminti na Dangote ya karrama ma’aikata 10 da suka nuna bajinta a aikinsu da kuma himma wajen kiyaye tsaro.

Daga cikin waɗanda aka karrama, Ismaila Suleiman ne ya zama direban da ya fi nuna ƙwazo da bajinta a shekarar da ake nazari a kanta.

Previous Post

Kamfanin Simintin Dangote Na Gboko Ya Ware Miliyoyin Naira Domin Tallafin Karatu Da Ƙarfafa Matasa

Next Post

Tinubu Ya Yaba Wa Kamfanonin Dangote Bisa Gudunmawa Ga Bunƙasar Tattalin Arzikin Nijeriya

Related Posts

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026
Kasuwanci

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

November 26, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya
Kasuwanci

Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

November 25, 2026
Kasuwanci

Ba Wani Kudin Daya Bace Ko Ba A Biya Ba Ko Ba A Lissafa Shi Ba – NNPC Ta Yi Karin Bayani

November 25, 2026
Shugabannin Masana’antu Sun Yabawa Dangote Kan Tasirin Noma A Afirka
Kasuwanci

Shugabannin Masana’antu Sun Yabawa Dangote Kan Tasirin Noma A Afirka

November 19, 2026
Kasuwanci

NNPC Ta Tabbatar Da Tashin Gobarar A Wani Gidan Mai Da Ke Jihar Legas

November 17, 2026
Makon Ɗorewa: Kamfanin Simintin Dangote Na Obajana Ta Tallafawa Ƙananan Masana’antu Da Yan Kasuwa
Kasuwanci

Makon Ɗorewa: Kamfanin Simintin Dangote Na Obajana Ta Tallafawa Ƙananan Masana’antu Da Yan Kasuwa

November 9, 2026
Next Post
Tinubu Ya Yaba Wa Kamfanonin Dangote Bisa Gudunmawa Ga Bunƙasar Tattalin Arzikin Nijeriya

Tinubu Ya Yaba Wa Kamfanonin Dangote Bisa Gudunmawa Ga Bunƙasar Tattalin Arzikin Nijeriya

Dangote Da NASCON Sun Buƙaci A Ƙara Zuba Jari A Masana’antu Domin Bunƙasa Tattalin Arziki

Hotuna Masu Ban Sha'awa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Trending
  • Comments
  • Latest
“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

“Sayen Wayoyin Hannu Na Zuwa Da Mummunar Matsala” — Abubakar Ubale

January 18, 2026
TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

TARON OPEN MIC WITH SHINE YAFARA YUNKURIN FARFAƊO DA ƊABI’U: MASU JAWABI SUN YABI HANGEN NESAN MR. SHINE

June 20, 2026
BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

BA Zamu Sake Yarda ayi Watsi da Matasa Bayan Zabe ba Inji Kungiyar NYA

January 28, 2026
ADC ta samu babban jigo na siyasa Farfesa Sani Bello don aikin duba kundin tsarin mulki bayan Awanni 24 da barin APC

ADC Ta Nuna Sabuwar Zamanin Gaskiya da Aminci ta Hanyar Nada Farfesa Mohammed Sani Bell

January 8, 2026
Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

Sanata Anthony Yaro Ya Gamsu Da Dokar Cin Zarafin yara

0
Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

Zamu Fara Bincike A Kan Matuka Jiragen Sama Don Hanasu Shan Kayan Maye, Inji Sanata Buhari Abdulfatah

0
Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

Kudirin Dokar Cibiyar Hukumar EFCC Ta Tsallake karatu Na Biyu

0
Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

Yan Majalisa da Ma’aikatar Yan Sanda sun goyi bayan kashi 15% na Mata Wurin daukar aiki

0
NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

NASCON Za Ta Gabatar Da Sabbin Kayan Dandano Na Dangote A Bikin Baje Kolin Kasuwanci Ta Kano Na 2026

November 26, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

Kamfanin Simintin Dangote Ta Ƙara Matakan Kiyaye Hadurra A Hanya

November 25, 2026

Ba Wani Kudin Daya Bace Ko Ba A Biya Ba Ko Ba A Lissafa Shi Ba – NNPC Ta Yi Karin Bayani

November 25, 2026
NNPC Ta Lashe Kyautar Duniya Ta Ƙungiyar WBA Bisa Kyawawan Ayyukanta A Fannin Sayar da Man Fetur

NNPC Ta Lashe Kyautar Duniya Ta Ƙungiyar WBA Bisa Kyawawan Ayyukanta A Fannin Sayar da Man Fetur

November 22, 2026

Recent News

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Kewaya Site

  • Gida
  • Game da Mu
  • Tuntuɓar
  • Advertise
  • Privacy & Policy

Biyo Mu

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Kasuwanci
    • Noma
    • Mai da Iskar Gas
  • Al’adu da Fasaha
    • Kirkire-kirkire
    • Tafiye-tafiye
  • Fashin Baki
  • Hotuna masu ban Sha’awa
  • Ƙasashen Duniya
  • Wasanni

© 2025 Kasuwancin Duniya - Wanda ya tsara AuspiceWeb.

Powered by CookieAdmin
Necessary cookies enable essential site features like secure log-ins and consent preference adjustments. They do not store personal data.
None
Functional cookies support features like content sharing on social media, collecting feedback, and enabling third-party tools.
None
Analytical cookies track visitor interactions, providing insights on metrics like visitor count, bounce rate, and traffic sources.
None
Advertisement cookies deliver personalized ads based on your previous visits and analyze the effectiveness of ad campaigns.
None
Unclassified cookies are cookies that we are in the process of classifying, together with the providers of individual cookies.
None
Powered by CookieAdmin