Daga Bashir Bello, Abuja
Kamfanin Simintin Dangote, reshen masana’antarsa da ke Gboko a Jihar Benuwe, ya bayar da tallafin karatu na miliyoyin naira ga ɗaliban manyan makarantu da na sakandare daga al’ummomin da ke kewaye da masana’antarsa guda shida.
Baya ga tallafin karatun, kamfanin ya kuma raba kayan fara sana’a, kayan aiki da takardun shaidar kammala horo ga matasan da suka kammala shirin ƙarfafa matasa.
Manufar shirin ita ce taimaka musu su kafa sana’o’insu, su yi amfani da ƙwarewar da suka samu yayin horo, tare da dogaro da kansu ta fuskar kuɗi.
Ministan Bunƙasa Ma’adinan Ƙasa, Dakta Henry Dele Alake, ya yaba wa kamfanin bisa shirye-shiryen ci gaban al’umma da yake aiwatarwa.
Ya kuma yi kira ga sauran kamfanoni masu zaman kansu da su yi koyi da irin wannan yunƙuri domin inganta rayuwar al’ummomin da ke kewaye da wuraren ayyukansu.
Alake, wanda Injiniya Achi Gregory, jami’in kula da ma’adinai na Ma’aikatar Bunƙasa Ma’adinan Ƙasa Mai Ƙarfi ta Tarayya a Jihar Benuwe, ya wakilta, ya buƙaci kamfanin ya ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen ci gaban al’umma da aka amince da su tare da al’ummomin da ke karɓar bakuncin masana’antarsa.
Da yake jawabi a wajen bikin raba tallafin, shugaban sashen kula da walwala da ci gaban al’umma na kamfanin Dangote Cement, Wakeel Olayiwola, ya ce aiwatar da yarjejeniyar ci gaban al’umma na nuna ƙudirin kamfanin na bai wa matasa ƙwarewa da kayan aikin da za su taimaka musu wajen kafa sana’o’i, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummominsu.
Olayiwola, wanda Dakta Johnson Kor, shugaban sashen kula da walwala da ci gaban al’umma na masana’antar Dangote Cement ta Gboko, ya wakilta, ya bayyana cewa tallafin karatu da shirin ƙarfafa matasa sun zo ne bayan wasu shirye-shiryen da kamfanin ya aiwatar, ciki har da shirye-shiryen tallafa wa manoma da mata.
Mukaddashin daraktan masana’antar Dangote Cement ta Gboko, Injiniya Arbind Singh, ya ce tallafin karatun da ake bayarwa duk shekara ga ɗalibai marasa ƙarfi daga al’ummomin da ke kewaye da masana’antar shaida ce ta yadda kamfanin ke sauke nauyin da ke kansa na taimaka wa al’umma.
Singh, wanda babban manajan samar da kayayyaki na kamfanin, Injiniya Tabershima Soom, ya wakilta, ya ce masana’antar ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa mata 150 da kuma shirin tallafa wa manoma 50.
Ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin ƙarfafa mata, an bai wa mata kuɗaɗen tallafi domin bunƙasa sana’o’insu, yayin da aka tallafa wa manoma da kayan aikin gona domin inganta ayyukan noma da samar da abinci.
Al’ummomin da suka amfana da waɗannan shirye-shirye sun haɗa da Tse-Kucha, Quarry, Amua, Mbazembe, Mbatur da Pass Brothers.
Da take magana a madadin Antoni Janar na Jihar Benuwe, shugabar Kwamitin Kula da Ma’adinai da Muhalli na jihar (MIREMCO), Lauya Dooshima Orosaga, ta yaba wa kamfanin bisa bin yarjejeniyar ci gaban al’umma. Ta kuma buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da sauran al’ummomin da ke kewaye da masana’antar su yi amfani da damar da aka ba su yadda ya kamata.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gboko, Yina Elias, ya ce gwamnati za ta ci gaba da bai wa kamfanin goyon bayan da ya dace domin ya samu nasarar gudanar da ayyukansa. Ya bayyana Dangote Cement a matsayin kamfani abin koyi wajen sauke nauyin da ke kansa na tallafa wa al’umma.
Shi ma shugaban gargajiya na gundumar Ukpekpe, Cif Tsegba Igbarumun, ya yaba wa masana’antar ta Gboko bisa gudummawar da take bayarwa wajen inganta rayuwar al’umma. Ya tabbatar wa kamfanin cewa al’ummarsu za ta ci gaba da ba shi goyon baya.
Igbarumun ya ce al’ummar yankin na daraja kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu da kamfanin, wadda ke amfanar ɓangarorin biyu, kuma za su ci gaba da tallata ayyukansa na alheri.
A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da shirin ƙarfafa matasa, Ignatius Aondohemba, ya gode wa kamfanin bisa tallafin da ya bayar. Ya yi alƙawarin amfani da ƙwarewa da kayan aikin da aka ba shi wajen kafa sana’ar da za ta bunƙasa har ya iya ɗaukar wasu mutane aiki.



















