
Daga BAshir Bello, Abuja
Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa Rukunin Kamfanonin Dangote bisa gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, yana mai cewa manyan jarin da kamfanonin suka zuba a muhimman sassa sun taimaka wajen ƙara yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, samar da ayyukan yi, rage dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje, kiyaye kuɗaɗen waje da ƙarfafa masana’antu a Nijeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya kai ziyara rumfar baje kolin Rukunin Kamfanonin Dangote a taron ƙoli na tattalin arzikin Nijeriya karo na 32, wanda ake gudanarwa a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilce shi a wajen taron.
Tinubu ya yaba da yadda rukunin kamfanonin ke gudanar da harkokinsa, yana mai jaddada muhimmancin jarin da kamfanoni masu zaman kansu ke zubawa wajen faɗaɗa ƙarfin samar da kayayyaki, raya harkokin tattalin arziki da tallafa wa ci gaban ƙasa.
Rukunin Kamfanonin Dangote na da jarin kasuwanci a masana’antun siminti, samar da takin zamani, tace sukari, sarrafa gishiri da tace ɗanyen man fetur.
Waɗannan jarin na taimakawa wajen ƙara wa albarkatun cikin gida ƙima ta hanyar sarrafa su zuwa kayayyakin da ake amfani da su, samar da ayyukan yi da bunƙasa hanyoyin samar da kayayyaki a cikin ƙasar. Haka kuma, suna taimakawa wajen rage dogaron Nijeriya ga kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Shugaban ya ce gwamnatinsa na samar da yanayin da zai ba gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu damar zuba jari, faɗaɗa harkokinsu da samar da ayyukan yi masu amfani ga tattalin arziki.
An bayyana cewa Rukunin Kamfanonin Dangote shi ne kamfani mafi ɗaukar ma’aikata a Nijeriya a ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu, inda Gwamnatin Tarayya ce kaɗai ta fi shi ɗaukar ma’aikata.
An gudanar da taron ƙolin tattalin arzikin Nijeriya na shekarar 2026 ne ƙarƙashin taken “Ci gaban Tattalin Arziki Mai Amfanar Jama’a: Samar da Ayyukan Yi, Ƙara Ingancin Samar da Kaya da Wadata Ga Kowa.”
Shugaba Tinubu ne ya buɗe taron a hukumance, inda ya kare sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa, tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin ma’aikata da masu ɗaukar aiki, da kuma bunƙasa tattalin arziki ta hanyar jagorancin kamfanoni masu zaman kansu.
Taron ya haɗa masu tsara manufofi, shugabannin kamfanoni, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen hanzarta bunƙasar tattalin arziki, inganta yawan amfanin aiki, samar da ayyukan yi da tabbatar da cewa jama’a da dama sun amfana daga ci gaban tattalin arzikin ƙasar.
Yabon da Shugaba Tinubu ya yi wa Rukunin Kamfanonin Dangote na nuna muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wajen gina tattalin arzikin Nijeriya mai ƙarfi, gasa da juriya ga ƙalubale.
Tinubu ya ce Nijeriya ta daɗe tana kasa cimma cikakken ƙarfin da tattalin arzikinta zai iya kaiwa, amma ya jaddada cewa babu wata hanya ta gajeren zango da za a bi domin cimma ci gaban tattalin arziki.
“Mun zo ne domin sake rubuta tarihin ƙasar da ta daɗe ba ta kai matsayin da ƙarfin da take da shi zai iya kai ta ba,” in ji shi.
Ta hanyar zuba jari a muhimman masana’antu, Rukunin Kamfanonin Dangote na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin mayar da Nijeriya ƙasa mai ƙarfin masana’antu. Ayyukansa na da damar ƙara bunƙasa sarrafa kayayyaki a cikin gida, ƙarfafa hanyoyin samar da kayayyaki da tallafa wa manyan manufofin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Baya ga haka, faɗin fannoni da kamfanonin Dangote ke gudanar da harkokinsu ya ba su damar kafa ƙaƙƙarfan matsayi a muhimman sassan tattalin arziki, inda suke samar da kayayyaki da ayyukan da ke tallafa wa gine-gine, noma, masana’antu, makamashi da sauran harkokin samar da arziki.
Ɗaya daga cikin manyan jarin rukunin kamfanonin shi ne katafaren matatar man fetur da masana’antar sinadaran man fetur ta Dangote da ke Legas. Ana sa ran matatar za ta sauya fasalin ɓangaren sarrafa da rarraba man fetur a Nijeriya ta hanyar ƙara ƙarfin tace mai a cikin gida da rage dogaro da shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.



















